MACE TA GARI 02


(MACE TA GARI 2)

24th/Dhul Hijjah/1442AH-3rd/August/2021

13. Mace ta Gari Itace Wacce Bata Raina Duk Wani Abu Wanda Mijinta Ya Kawo mata,
14. Mace ta Gari itace Wacce Bata Ɗaurawa Mijinta Abinda Yafi Karfinsa,
15. Mace ta Gari itace Wacce Bata Hangen Abinda Mazajen Wasu Sukeyimusu tace Mijinta Sai Yayimata shi koda kuwa Bashi da Halin yin Hakan,
16. Mace ta Gari itace Mai Ƙarfafawa Mijinta Ƙwarin Gwuiwa a Duk Lokacin da taga Yana Ƙoƙarin Karayar da Zuciyar sa,
17. Mace ta Gari itace Mai Ƙoƙarin ta Kwantarwa Mijinta Hankali Akoda Yaushe,
18. Mace Tagari itace Mai Ƙoƙarin Ɓoye Duk wata Damuwar ta Sabida Kar Mijinta Ya Shiga Wani Hali,
19. Mace ta Gari itace Mai Ƙoƙarin Tat'tala Dukkan Wani abu Wanda Mijinta ya Mallaka Komae Arzikinsa Bazata Taɓa Ɓarnatarwa ba,
20. Mace ta Gari itace Mai Mutunta iyayen Mijinta Tamkar Nata,
21. Mace ta Gari itace Mai Daraja Dangin Mijinta Batacin Zarafinsu,
22. Mace ta Gari itace Mai Taimakawa Mijinta Wajen Tarbiyyar Yaransu, Domin Bazata Taɓa Cewa Yaranta Sunfi Ƙarfinta ba, Balle Kuma tace Yazatayi Dasu,
23. Mace ta Gari itace Mai Baiwa Mijinta Hakuri Aduk Lokacin da Tayi Masa ba dai dai ba,
24. Mace ta Gari itace Mai Yafiya ga Mijinta Aduk Sanda Yaɓata Mata rai ko Yayimata Wani abu da ba dai dai ba,
25. Mace ta Gari itace Mai Ɗora Mijinta Akan Turbar Gaskiya,
26. Mace ta Gari itace Mai Kallon Mijinta a Matsayin Sarki Wadda Yafiyemata Komae Awajenta,

Zamu Dakata Anan, Zamuci Gaba Inshaa Allaah,

Allaah Yazaɓamana Mataye Nagari, Suma Matan Yazaɓamusu Mazaje Nagari,

Daga Ɗan Uwanku A Musulunci

(Ustadh_Abulfawzhaan)

Post a Comment (0)