MIJIN ƘAZAMA 02

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

      
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀    
           *MIJIN KAZAMA*
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
        🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

             *Na*                            

          *Maman Hafiz* 
        
                  *Niger*

   *Wannan page din naku ne group din Mijin Kazama Fans*


*Bismillahi Rahamani Rahim*


*Page 2*

Mama tashi ta yi, ruwan wanka ta kai masa douche sahani (buta) ta cika, ajiye masa wajen alwala ta yi. Abinci ta dauko ta ajiye, juya ta yi ta dauro alwala lokacin Magriba ya gabato bayan ta gama dakin su Amina ta leka ta ce da su fito su yi alwala su yi salla 

Lokacin Hanane ta gama karatun Alqur'ani, waya ce a hannunta WhatsApp take da kawayenta 'yan ajinsu. Amina ma chatting take yi da wani saurayinta da ta hadu da shi a Facebook. Ajiye Wayoyin suka yi a tare, suka fito daga dakin lokacin Babansu ya fito yana alwala gaishe sa suka yi ya amsa bayan ya gama masallaci ya fice 


Washegari bayan sun gama sallar Asuba, Hanane ta fice cuisine (dumame) petit déjeuner ta daura. Ta share tsakar gidansu madaidaici, ta yi wanke-wanke ta yi wanka ta shirya. Amina kuwa sai 7:00 ta fito, dauraye jikinta kawai ta yi da ma ita wanka bai dame ta ba, sai tayi sati biyu ba ta yi ba wanka sau guda ba. KAZAMA kawai! 😌 Mai ta shafa tayi kwalliya ta saka tenu. Bayan sun karya suka je suka gaishe da iyayensu.
  
Fiyewa sukayi daga gidan suna sauri-sauri sun kusa makara suna isa école kowacce ta classe dinsu ta nufa. Amina na shiga classe aka dau shewa ga miss ga miss *(ni kuwa nace ina miss jiki da warin dauda, baki na wari🤣🤣)*

Zaune ta yi kusa da Zainab bencinsu daya, ita kuwa Zainab da kyar take iya zama da Amina daurewa kawai ta yi. Zama da Amina sai an dage 🤣🤣 ga warin dauda ga warin baki. ( Gaskiya su Amina an ji kunya😅) Amma fuska kyal da ita an sha kwalliya. 😅😅 

Abu guda yasa take zama da ita, Amina ke gwada mata duk wata jarabawa da suke yi, Zainab ba ilimi kamar ita ce...🙊

Monsieur (teacher) ya shigo classe ta yi shiru, cour (lacca) ya fara, tambayoyi ne ya fara jerowa. Aji ya yi tsit Amina ce ke basa amsa *(Amina akwai illimi toujours c elle la première de sa classe)* ita ce kullum ta farko, a kowacce jarabawa.

Bayan sun fito récréation a classe ta zauna ta fito cahier ta fara révision,

Monsieur (teacher) da zai shigar musu a gaba jarabawa ce zai musu. Tana karatunta, Hanane ta shigo aji "ya6 Amina na tafi gida mun tashi " Kai ta daga mata alamar to, juyawa ta yi ta fice abinta.

Bayan ta gama zana jarawava (devoir ) sai da ta jira Zainab tare suka taho da ita layinsu daya,m

*Garin Niamey*
 
Kwance yake kan laulausar katifa yana danna ordinateur ( lafto), wani aiki ne da bai gama ba tun a Bureau(office) yake son ya kammala, yana yi yana kurba shayi don barci yake ji ga shi bai karasa aikin ba.

Turo porte (kofa) da aka yi yasa shi juyawa ya ga ko wane ne? Momynsa ce ya gani sanye da gilashi a idonta. Sallama ta yi ya amsa ta ce, "Abubarcar ba ka yi barci ba? Na zata ai ka kwanta."

"Momy ban yi ba, yana so dai ya dauke ni wani aiki ne nake son na kammala kafin na kwanta, ina daddy?"

Ta ce, "Ya yi barci. Maganar yarinyar da na maka ce nake son ka je ka gan ta, idan ta yi ma sai ku daidaita ka san ba zan maka dole ba. Haka ma daddynka ya ce sai kana son ta za ka aure ta."

Dago kansa ya yi cikin shawagaba ya ce, "Momy ai ko ba na son ta tunda zabinki ce shike nan zan aure ta." 

"A'a Sadik ba zan maka dole ba, sai ka amince da ita."

Mikewa ta yi, "Ka ci gaba da aikin ka zan koma sashenmu, mu kwana lafiya." Ta fice daga dakin nasa ta nufi sashensu


*Maman Hafiz* ✍️

Post a Comment (0)