MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASA BAYA?

27. MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASA BAYA?


Tambaya:
Assalamu Alaikum, Allah ya haɗa ni da miji mazinaci, shin idan na daina haɗa shimfiɗa dashi don gudun ɗaukar wani ciwo ina da laifi?

Amsa:
Wa alaikum assalam, abinda yafi shine ki yiwa magabatansa bayani, don su tsawatar masa ya daina, in kuma kin tabbatar ya ɗau cutar Sida kina da damar da za kije wajen Alƙali don ya raba auren, tunda musulunci yayi umarni da tunkuɗe cuta gwargwadon iko, in har miji yana ciyar da matarsa to ya wajaba ta amsa kiransa, wannan yasa ɗaukar matakin hanashi kanki zai iya jawo muku rigima. Sanya Alƙali ko magabata a rikicin shine daidai.
Allah shine mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Post a Comment (0)