UWAR MIJI // 1

UWAR MIJI // 1


.
MA'ANAR KALMAR
Idan aka ce uwa a harshen Hausa ana nufin babba da wasu qanana suka fita daga cikinsa, kamar dai a ce uwar-gwaza ko uwar-garke, ko wanda qananan suka qare gare shi kamar uwar-hanji, ko inda ya fi mahimmanci a cikin makamantansa kamar uwar-daka, ko shugaba a rukunin mata da ake kira da uwar qungiya, ko jagorar wani uwar-daki, amma a ma'ana uwa na nufin mahaifiya, wace ta dauki ciki na tsawon watannin da jariri zai isa haihuwa kuma ta fitar da shi, uwa kenan da ake mata laqabi da ma-ba-da nono.
.
A mutane wata kan sha wahala tun samun cikin har zuwa haihuwarsa, da yawa mata kan ce cikin da-namiji ya bambanta da na diya-mace wajen laulayi da jijjiga, bar batun amai da tashin zuciya akwai allurori da magunguna har da jiqe-jiqe da uwar kan yi ta fama da su, wata matar dalilin kamuwarta da hawan jini kenan har mutuwa, wata kuma ciwon sikari, wata na zuciya da sauran mayan cututtuka, akwai wace cikin kan yi ajalinta, da ta haifo shi ta kwanta-dama, wata ma da cikin take tafiya.
.
Wannan wahalhalu ba iyakarsu kenan ba, kusan dan-ba aka dora, domin daidai lokacin da za a haifo shi wani babban tashin hankali ne, kashi ma kenan in yayi kauri yakan wahalar, to bare da mai kai da kafada, shi ya sa wasu matan sai an qara su, in sun haihun kuma a dinke su kamar buhuna, wasu ma haihuwar ta gagara sai dai a barke cikin a zaro yaron, kowanne dai jini kan kwarara, da yawansu sai an qara musu.
.
Bayan haihuwar kuma sai jinyar wurin, shi ma wani tashin hankalin ne, wasu matan ma sun fi alhinin biqinnan sama da komai, rushi, ruwan zafi ga duka da ganye kamar wace ta yi qazafi, wasu sun fara karbar allurori kenan sai yadda hali ya yi, uwa kenan, a sha'anin ciki, haihuwa da raino ba abinda yake da sauqi, da yawa mu maza in aka ba mu jaririn ma duk mu qosa a karbe shi mu qara gaba, masu qarfin hali ma har fada suke yi wai an bar yaro yana kuka, bayan ba uwar ce da shi ita kadai ba.
.
A kullum yana nanuqe da ita, a hannu ko a baya, fitsari, kashi, tumbudi da sauran qazanta duk ita ce, tun daga haihuwa har zuwa lokacin da za a nemo masa qani ko qauna, kusan duk abubuwan da aka lissafo dinnan uwa ke shansu kuma take fama da su, na sha ganin uwa ta sa bakinta a hancin jaririnta ta jawo majina ta tofar, don dai ya sami damar shaqar numfashi, duk fa a lokacin ita ma tana fama da jinyar haihuwar.
.
Kowace mace ta san jigila da haqilon da kowace uwa take fama da shi a kan jaririnta, da yawansu ba sa iya barci, saboda kukansa, ga tsotso na tashin hankali, wata sai ta sha wasu abubuwan marasa dadi don dai nonon ya zo ta sami abinda za ta ba wa yaron, in bai jin dadi ita ma hankalinta a tashe, wani sa'in tare suke kuka da yaron ba wanda ya sani saboda tausayi da fargaba.
.
Ba uwar dake da kwanciyar hankali in ba ta ga yaronta ya sami lafiya ba, wasu magungunan da yaron ke buqata sai dai ita ta sha, yaron ya samu a nono, ba ta iya minti 10 in ba ta ji shi a jikinta ba, sabanin uban da ba ya iya minti goma tare da shi a jikinsa, qila shi ya sa wani mawaqi yake cewa "Uwa uwa ce ba kowa ke amsa sunan ba" don duk kyautatawar da wata za ta yi maka to bayan wannan ne.
.
Ko uwaye maza ba sa iya jurewa, akwai uban dakan dunqufa yaron da bai gama iya zama ba don ya tsula masa fitsari, wani ma a kan uwar zai qare sai ka ce ita ta yi masa, an saki mata da yawa da sunan suna nuna ko-in-kula da riqon yaran, bayan uwayensu maza a daidai wannan lokacin ba abinda suke yi, kuma sun fi kowa taqama da cewa yaron nasu ne.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga
MIFTAHUL ILMI
_____

TELEGRAM MEDIA⇨https://t.me/miftahulilmii

TELEGRAM⇨https://t.me/Miftahulilm2​

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Post a Comment (0)