ZAN IYA ZUWA JANA'IZAN WANDA BA MUSULMI BA?

ZAN IYA ZUWA JANA'IZAN WANDA BA MUSULMI BA?


:
*TAMBAYA*❓
:
Menene hukuncin musulmin da ya tafi jana’izan wanda ba musulmi ba, a gida ko a Coci sannan da taya su zaman gaisuwa, ko da ‘sun hada ‘yan'uwantaka da su?
:
*AMSA*👇
:
 Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Musulunci addini ne mai kyautatawa kowa, kuma zaman tare yana lazimtawa Musulmi wasu hakkoki na makwabtaka da zamantakewa ga abokan zama, Musulmai ko Kafirai, Kiristoci, Yahudawa, Mushirikai da sauransu. Zaman tare ya Farlatawa Musulmi ga abokan zamansa (ko ba Musulmai ba ne), taimakon juna, tausayawa, jajantawa, taya murna,
gaisuwa, Nasiha, kariya, tsare hakki da dukkan kyautatawan da bai kaucema Shari’ah ba.

Malamai sun ce babu wani Nassin da yahana Musulmi bin Jana’izar wanda ba Musulmi ba. Abinda Nassi yahana shi ne yimasa Sallah ko addu’a, Wannan kam haramun ne da Nassin Al-Kur’ani. Malamai sun samu saɓani dangane da Jana’izar wanda ba Musulmi ba, sun bada hukunci kamar haka:

1 – Haramci: wato Haramun ne halartar Jana’izar mutumin da ba Musulmi ba ne ga Musulmi. Sun kafa hujja da cewa Jana’iza tayi kama da Sallah ko Addu’ah wanda Allah ya Haramta. Wannan shi ne fatawar Imam Muhammad Ibn Usaimin da wasu malaman Malikiyya.

2 – Halacci: wato Halal ne kuma babu laifi Musulmi ya tafi Jana’izar Kafiri. Sunkafa hujja da wasu Hadisan magabata (ATHAR) cewa Sahabai dayawa sun tafi Jana’izar Ummul-Harith Bin Abi-Rabi’ah kuma ita Kiristace. Tafiya Jana’izar Kafiri abu ne mai kyau idan akwai wata Maslaha a cikin haka. Wannan shi ne Fatawar malaman Shafi’iyya, Hanafiyya da Imam Ahmad.

3 – Halacci bisa sharadi: Babu laifi Musulmi ya tafi Jana’izar Kafiri indan dan-uwansa ne na kusa, kuma ya koma chan gefe kada yayi tarayya dasu cikin abinda suki yi. Kuma da sharadin babu wani abinda ake bin Jana’izar da shi wanda ya Saɓawa Shari’ah.

4 – Babu laifi Musulmi yayi Ta’aziyya da jajantawa ga Kafiri, Musulmi zai yi Ta’aziyya da kalmomi kamar: Allah ya maida muku alkhairi, Allah yaba ku Hakurin rashin dan-uwan ku, Allah ya tabbatar muku da alkhairi, Allah ya hadashi da sakamakon ayyukansa… etc. Amma fa kar ya kuskura yayi addu’ar gafara, rahama… etc ga mamacin.

5 – Babu laifi Musulmi ya ziyarci kabarin dan-uwansa Kafiri amma fa ba zai masa addu’ah ba.

6 – Babu laifi shiga Coci don Ta’aziyya, Jajantawa, Saurarar wasu karatuka (seminar, workshop, symposium … etc). Amma musulmi ya kiyaye kada yayi duk wani nau’in ibada da suke yi. Sai dai abinda yafi shi ne kar Musulmi ya shiga Coci sai indan ya zamo dole kuma yayi takatsantsan.

ALLAH SHI NE MAFI SANI.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)