JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 10


JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 10
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
ANNABI YUSHA' AS
Shi ne muke kira Yusha'u da Hausa, wasu qabilun su ce masa "Joshua" gaskiya a kan sanya wa yara sunan banu Isra'ila sai dai ban ga musulmai na qin sunansu kamar Yusha'u ba, har ma an sami sabani ko zai yiwu mu iya saka wa diyoyinmu sunan ko a'a? Yahudawa bisa dabi'arsu sun liqa masa munanan abubuwa wadanda bai dace a ce annabin Allah yana aikata su ba, ko a musulman ma wasu na tantamar cewa manzon Allah ne ko salihi ne kawai, bisa hujjar cewa tunda banu Isra'ila suka saba wa annabinsu aka bar su ba a sake aiko musu wani manzo ba sai da suka ji jiki na tsawon shekara arba'in.
.
Suka ce in haka ne zai yi wahala a ce Yusha'a AS manzo ne, don ya yi zamani da Musa AS, sai dai akwai wani abin kula a cikin hujjar tasu ma, domin annabi Yusha'u AS shi ne matashin nan da Annabi Musa AS ya hau jirgi tare da shi wanda Qur'ani ya kawo qissarsu doguwa da abubuwan da suka riqa gani, {وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِفَتَاه} (Yayin da Musa ya ce wa yaronsa) akwai wani hadisi ma na Muslim 2380, wanda yake cewa (( ثُمَّ انْطَلَقَ هُوَ وَفَتَاهُ يُوشَعُ بْنُ نُونٍ ، حَتَّى إِذَا أَتَيَا الصَّخْرَةَ وَضَعَا رُءُوسَهُمَا )) (Sai suka kama hanya shi da yaronsa Yusha'u dan Nun har sai da suka zo wurin wani dan dutse suka dora kawunansu...)
.
Matuqar yana qarami ne a wannan lokacin zai yuwu banu Isra'ila su sha wahalar shawagi a Sina na tsawon shekaru 40 din kafin Allah SW ya kubutar da su a hannunsa, ko tun farko dama ba watsuwa suka yi a duniya ba, suna nan zube a wuri guda, wato tsakanin Masar da Palestine ba wata shiriya ta manzanci saboda abin da suka aikata, sai lamuransu suka koma hannun manyan gidajen nan guda 12 da Musa AS ya raba musu.
.
Yusha'u AS annabi ne cikin Annabawan bani Isra'ila da ya karbi ragamar annabci bayan gushewar Musa AS, kuma shi ne ya harhado kawunan banu Isra'ila gida 12 din qarqashin jagoranci guda wanda samuwar hakan suka iya hada rundunar da za ta yi yaqi har dai suka iya kai wa Palestine babban harin da a qarshe suka bude ta da qarfi ta zama qasar muslunci, an yi musu alqawarin shiga tun farko tare da Musa AS ba tare da yaqi ba amma suka juya baya tare da kawo hanzarin da zai hana su shiga, yanzu ga shi za su shiga din cikin yaqi ma, har ma wasu da dama a cikinsu sun mutu a dalilin yaqin, sai dai a qarshe nasara ta tabbata a hannunsu sun shiga bigire mai tsarkin da suka kwashe shekaru suna nema.
.
Annabi Yusha'u AS ya riqa kiran mutanensa zuwa ga Allah, yana tsoratar da su matsalolin sha'awe-sha'awe, da nisantar qeta, kamar yadda ya tsoratar da su nisantar duk wata hanya ta shedan, ya dora su a turba ta qwarai yadda muslunci zai yi rinjaye, qissarsa ta bude qasar Ibraniyya sananniya ce, akwai ta a Masnad 14/65 na Imam Ahmad, Ibn Kasir ya kawo ta a Albidaya wannihaya 1/301, Ibn Hajar a Fathul Bari ya inganta qissar 6/255, Albani ma ya ce ta inganta a cikin Silsila 2226.
.
Wato bayan runduna ta gama cika sai aka doshi wurin yaqi aka kama gadan-gadan, nasara na tare da banu Isra'ila sun bude wurare da dama amma maraice ya yi rana na gab da fadawa a ranar Juma'a, ma'ana kashegari Asabar kenan, banu Isra'ila ba sa farauta a ranar saboda girmama ta, don haka suka nemi Annabi Yusha'u ya roqa musu Allah don ya jinkirta fadawarta, Annabin Allah ya roqa musu kuma Allah ya biya musu buqata, ranar ta yi jinkiri har suka sami damar cin nasara. To sai dai ba shi kenan ba, bayan sun sami damar shiga qasar sai suka ci gaba da barnarsu, suka kashe annabawansu, suka koma hannun sarakunansu.
.
Sai ya zamanto babu shiriya tare da su, sarakunan da ke tsakaninsu giyar sarauta ta yi ta dibarsu don haka suka yi ta gasa musu gyada a hannu, suka riqa gamuwa da nau'o'i daban-daban na azaba, to dama akwai sauran abubuwan da Musa AS ya bar musu, kamar akwatinsa da suka riqa neman tabarraki da shi, amma saboda sabawan da suka yi da barin hanya madaidaiciya ba su yi nasara a yaqoqin da suka shiga da mutanen Gazza da Asqalan ba, aka yi nasara a kansu aka kore su daga garin bayan da suna murna sun sami qasar.
.
A dalilin haka suka fara duba kawunansu gami da nadamar abin da suka riqa aikatawa, sai suka nemi annabin wannan lokacin suka ce masa {ابْعَث لَنَا مَلِكاً نُقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ قَالَ هَلْ عَسَيْتُمْ إِنْ كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ أَلَّا تُقَاتِلُوا قَالُوا وَمَا لَنَا أَلَّا نُقَاتِلَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَقَدْ أُخْرِجْنَا مِنْ دِيَارِنَا وَأَبْنَائِنَا فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقِتَالُ تَوَلَّوْا إِلَّا قَلِيلاً مِنْهُمْ} (Ka zabo mana da wani sarki da za mu yi yaqi saboda Allah, ya ce ina gudun in aka wajabta muku yaqin ba za ku yi ba, suka ce: Ya ba za mu yi yaqin ba an kore mu daga gidajenmu da yaranmu, da aka wajabta musu suka qi yi sai 'yan qalilan).

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)