*MUGUN ABOKI...................*
👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬
*FUTOWA TA 👇*
*(8)*
*WANE NE ABOKI NA BANZA❓*
Aboki na banza shine mugun abokin da yake barin wani mummunan tabo daga cikin tabubbuka ajikin abokinsa, shi mugun aboki ba wai yana juyawa abokinsa dabi'a bane kawai, shine abokin da yake sabbaba muguwar cutarwa ajikin abokinsa yana sane ko baya sane da nufi ko ba tare da nufi ba, mugun aboki shine yake nunawa abokinsa mummunan tafarki, ya shiryar da shi zuwa ga aikata miyagun aiyuka kuma ya qarfafesa akai, kamar yadda idan ka zauna da aboki na kwarai zaka zama na kwarai, haka zalika zamanka da aboki na banza zaka zama mutumin banza irinsa, saboda haka larabawa suke cewa "الصاحب ساحب" ma'ana aboki yana mayar da abokinsa ya zama irinsa ta ko wacce fuska.
*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*
*MU HADU A FUTOWA TA 09*
*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibai masu neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
*(UMMU HANAN)*
🥏08026799975🥏