*MUGUN ABOKI...................*
👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬
*FUTOWA TA 👇*
*(9)*
*SIFFOFIN ABOKIN BANZA*
Akwai wasu siffofi wanda duk wanda ya siffantu dasu babu makawa ya shiga cikin jerin miyagun abokai siffofin sune kamar haka :
*1- Mummunar dabi'a* babban abun da yake bam-bamce tsakanin aboki na kwarai da aboki na banza shine mummumar dabi'a wajan kaikawowarsa da aiyukansa misalin shan taba, sata, shan miyagun kwayoyi, wadannan na daga cikin Siffofin da zaka gane mugun aboki dashi.
*2- SHAHARA DA MUGUN ABU A TSAKANIN MUTANE* shara da mugun abu a tsakanin mutane na daga cikin Siffofin da zaka yi sauri wajan gane aboki na banza dashi, aboki na banza yana shiga cikin tarihin al'umma ta yadda kowa wanda yake ke waye dashi zai dunga kyamatarsa, saboda ta'addancinsa acikin al'umma, saboda haka ya yin da zaka zabi aboki ka bibiyi maganganun mutane akansa domin babu abun da zai buya garesu dan gane dashi.
*3- KARYA DA YAUDARA* Aboki makaryaci baya kamata kayi abota dashi saboda bai zama nagari ba, karya na daga cikin Siffofin mafiya bayyana ga miyagu abokai, domin galibi karya na zama tsani garesa domin ya cimma burinsa da maslaharsa, zaka samesa zai maka karya kuma zai yiwa wasun Kama, zai yi amfani da yaudara domin ya cimma maslaharsa ko ya rufe munanan aiyukansa a gaban wasu har ya karbi abun da yake so, alokacin da gaskiya take kasancewa itace maslaharka zaka samesa kuma a gefanka, amma fa ka sani yana amfani da karya wajan da yawa daga cikin maslahohinsa, aduk lokacin da mutum wannan siffar ta bayyana agaresa babu makawa kayi qoqarin gudunsa domin ka tsira da rayuwarka.
*4- ABOKI MAI MASLAHA* yi qoqari wajan nisantar abokin da maslahar kansa ce agabansa, babu ruwansa da abokantaka face cikar maslaharsa, baza ka samesa wajan taimakamaka ba har sai idan yasan ta wannan hanyar maslaharsa zata cika, idan kaga yana taimakamaka to tabbas maslaharsa ta cika, da zarar wannan siffar ta bayyana ga mutum yi qoqari wajan nisantarsa.
*5- RASHIN AMANA* Amana na daya daga cikin manyan Siffofi ga aboki na kwarai, amma shi mugun aboki bazai taba yuwuwa amince masa a wani abu ba face sai ya ci wannan amanar, bazai taba boye sirrin ka ba, bazai taba kare alfarmar gidanka ba da iyalanka, bazai taba kiyaye maka kyakykyawan abun ka ba, don haka yi qoqari wajan nisantar wannan aboki daga duk kan abun da ya shafi rayuwarka.
*6-TSIRA DA KAI* aboki na banza ya yin da wata matsala ta taso muku yana qoqari wajan kubutar da iya kansa, idan na gudune ya gudu idan na magana ne ya yi qoqari wajan kubutar da iya kansa babu ruwansa da kai, kan sa kadai ya sani yi qoqari wajan nisantar wannan mugun aboki.
*7- HANI GA ALKHAIRI KIRA GA SHARRI* Aboki na kwarai na iya bakin qoqarinsa wajan taimakamaka ka canja miyagun halayenka, amma shi mugun aboki zai dunga yabonka bisa miyagun Siffofinka yasa ka dunga jin dadinsu ya saka ka karikesu gam, ya kusheka bisa kyawawan Siffofinka ya sa kabarsu yi qoqari wajan nisantar wannam abokin.
*8- HASSADA* gareka mai karatu mai daraja yi qoqari wajan nisantar duk abokin da hassadarsa ta bayyana domin babu Alkhairi a zama tare dashi, saboda ko da yaushe zai dunga qoqari wajan yaga ya nisantar da wannan ni'mar da Ubangiji ya yi maka daga gareka, yin abota dashi bara zana ne ga rayuwarka.
*9- KYETA* kyeta na daya daga cikin miyagun Siffofi mutum bazai siffantu da ita ba face ya zama mai hassada, kuma aduk lokacin da ya samu dama akan ka na iya turaka zuwa ga mahallaka mutuqar yaga ka samu abun da babu maslaharsa aciki ko amfaninsa.
*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*
*MU HADU A FUTOWA TA 10*
*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibai masu neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
*(UMMU HANAN)*
🥏08026799975🥏