INA SON CIKAKKEN BAYANI AKAN KUL'I !
Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Malam ina so amin cikakken bayani akan kul'i
Amsa
Wa alaikum assalam
Khul'i shi ne mace ta fanshi kanta daga wajan mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa mijinta à hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan musulunci.
Ya halatta à sharia Allah mace ta yiwa miijnta Kul'i in har ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa na aure ba, kamar yadda aya ta (229)a suratul BAKARA ta tabbatar da hakan.
À zance mafi inganci Kul'i yana saukar da saki daya, saidai yana nisanta mace da mijinta ta yadda ba zai iya saké zama da matar ba, sai in ya bayar da SADAKI sannan an kara daura sabon aure.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20/06/2017
Shin ya ake dafa ciccibi kuma akwai maganin da ake amfani dashi wurin dafawa
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteShukuran
Delete