WACCE TA YI TSARIN IYALI, IDAN AKA SAKETA, DOLE TA JIRA JINI UKU !

WACCE TA YI TSARIN IYALI, IDAN AKA SAKETA, DOLE TA JIRA JINI UKU !



Tambaya
Assalamualaikum
Malam macen da ba ta haila saboda planning na wasu watanni, yaya zata yi idan aka saketa?.
Allah ya Kara Ikhlasi

Amsa
Wa alaikum assalam
Za ta jira har ta ga jini uku, ko da kuwa za ta yi shekaru (30) Kamar yadda aya ta (228) a suratul Bakara ta Yi bayani.
Ina yiwa mata nasiha su nisanci yawancin magunguna da alluran tsarin iyali saboda suna sabbba Matsaloli.

Duk da cewa tsarin iyali na wucin gadi ya halatta, sai dai imani da cewa: kowanne abin haihuwa da arzikinsa yake zuwa yana da muhimmanci, saboda hakan zai sa kowa ya samu nutsuwa, ya daina tsorata da yawan yaran da zai haifa.

Allah ne mafi sani 

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
25/06/2022
Post a Comment (0)