TAFIYA TA KAMA NI A TSAKIYAR YINI, KO ZAN IYA KARYA AZUMINA ?
Tambaya :
assalamu alaikum. akramakallahu barka DA warhaka tambaya gareni, mutum ne zaije umara cikin azumi sai yazamana jirginsu zai tashi karfe biyu na ranan, shin kame bakine daga safe zuwa lokacin tashin KO kuwa bazaiyi azumi ba kwata kwata aranar?
AMSA :
Wa alaikum assalam, Zancen mafi yawan malaman Hanafiyya da Malikiyya da Shafi'iyya shi ne : idan mutum ya yi tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci ba, saidai idan ya shiga wahalar da ba zai iya jurewa ba, amma a wajan malaman Hanabila ya halatta, saboda Allah ya halattawa matafiyi cin abinci a suratul Bakara kuma bai banbanta tsakanin wanda ya yi tafiya a farkon yini ba, da wanda ya yi a tsakiya.
Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba : Al'insaf 3/205
Jamilu Zarewa
21\6\2015