WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN SAMA ?

WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN SAMA ?


Tambaya:
 Assalamu alaikum Allah ya karawa 
malam ilimi da fahimta. Shin da Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci?. Nagode malam.

Amsa
Wa alaikum assalam. To dan’uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa maganganu guda biyu :

*I.* Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada
salloli saboda ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa
da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila
kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF
2\340. 

*2* Bai halatta ga wanda bai je sallar
jam’i ba ya hada salloli saboda ruwan sama,
saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je
masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa,
wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don haka rahusar baza ta sameshi ba, sannan kuma shari’a ta yi nufin ta kiyaye sallar jam’i shi ya sa ta saukaka wajan hada
salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam’i ta tozarta, wannan ita ce maganar
Imamu shafi’i a littafinsa Al’umm 1\195, Afahimtata maganar karshe ta fi inganci, don haka wanda yake gida ba zai hada salloli ba.

Allah ne mafi sani

DR JAMILU YUSUF ZAREWA*
12/11/2015
Post a Comment (0)