WANENE MAHDIY KUMA YAUSHE NE ZAI BAYYANA?
TAMBAYA TA 2987
********************
Assalamu alaikum Malam an wuni lafiya, yaya karatu, yaya dalibai?
Malam nima dalibinka ne, ina bibiyar karatunka a facebooK.
Malam tambaya ce dani dan Allah Malam ina so ayi mun bayani wane ne Mahadi kuma yaushe ne zai bayyana malam dan Allah ayi min bayani nagode Allah ya kara illimi.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika hadisai da yawa sunzo da labarin zuwan Imamul Mahdiy wanda harma Malamai suna cewa yawan hadisan da kuma shahararsu yakai matsayain tawatur.
Daga cikin hadisan akwai ingantattu, akwai kuma raunana (wato Dha'eefai) amma bari in dan tsakuro maka daga wadanda malamai suka ce sun inganta :
1. Hadisin Nana Ummu Salamah (Allah ya yarda da ita) tace "Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa "HAKIKA AL MAHDIY ZAI FITO NE DAGA CIKIN ZURIYYATA (DAGA CIKIN NASABATA, DAGA IYALAN GIDANA) DAGA CIKIN 'YA'YAN FA'DIMAH"
ADUBA SUNANU ABI DAWUD, Juz'i na 11 shafi na 373.
2. Hadisin Abu Sa'eed Alkhudhriy (Allah ya yarda dashi) yace Manzon Allah ﷺ yace "ALMAHDIY DAGA GARENI YAKE, YANA DA MADAUKAKIN GOSHI, DA TSININ KARAN HANCI. ZAI CIKA QASA DA ADALCI DA KYAUTATAWA KAMAR YADDA AKA CIKATA DA ZALUNCI DA DANNE HAKKI, (ZAI ZAUNA) TSAWON SHEKARU BAKWAI".
ADUBA : sunanu Abi Dawud, kitabul Mahdiy juzu'i na 11 shafi na 375 hadisi na 4265.
MUSTADRAK NA HAKIM (Juzu'i na 4 shafi na 557).
3. Hadisin Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudhriy (Allah ya yarda dashi) yace : "Manzon Allah ﷺ yace "Almahdiy zai zo akarshen al'ummata, Allah zai shayar dashi ruwan sama kuma Qasa zata fitar da tsirranta za'a bayar da dukiya kuma dabbobi zasu yawaita, kuma al'ummah zasu gurma, kuma zai rayu ne shekaru bakwai ko takwas".
MUSTADRAK NA HAKIM (Juz'i na 4 shafi na 557 -.558)
4. Hadisin Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (karramal Lahu wajhahu) yace : Manzon Allah ﷺ yace "ALMAHDIY DAGA CIKINMU YAKE, MU AHLUL BAITI. ALLAH ZAI SHIRYASHI ACIKIN WANI DARE".
ADUBA : Sunanu Ibn Maajah juzu'i na 2 shafi na 1367
Atakaice dai Imamul Mahdiy mutum ne daga cikin zuriyar gidan Annabta (ahlul bait) kuma sunansa irin na Manzon Allah ne ﷺ hakanan sunan mahaifinsa da na mahaifiyarsa. Babu wanda yasan lokacin bayyanarsa sai Allah (SWT) Domin kuwa wannan yana daga cikin gaibu ne. Sai dai abinda wadannan hadisan ke tabbatarwa shine zai bayyana ne gan da tashin alqiyama bayan duniya ta cika da zalunci.
Kuma zai hadu da Annabi Eisa bn Maryam (alaihimas salam) harma zai jagoranci sallah wanda shi Annabi Eisa din yana yana daga cikin mamunsa awajen. Kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya fada acikin wani hadisi yace : "ACIKINMU (MU AHLUL BAITI) AKWAI WANDA ANNABI EISA 'DAN MARYAMU ZAIYI SALLAH ABAYANSA".
(Abu Nu'aym ne ya ruwaito hadisin acikin littafinsa mai suna Akhbarul Mahdiy) kuma albaniy ma ya ingantashi acikin Sahihul Jami'i hadisi na 5795.
Kuma bayyanarsa tana daga cikin alamomin kusantowar tashin Alqiyamah kamar yadda Malamai suka fa'da. Munyi imani da wannan Amma mu bamu kudurce irin abubuwan da Shi'a da Ahmadiyyah suka kudurce game dashi.
Daga karshe ina maka fatan dukkan alkhairi dakai da duk daliban Zauren Fiqhu, kuma ina addu'ar Allah shi tabbatar damu akan shiriya. Ameen.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 09/11/1443 08/05/2022)