*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*
_*Daga zauren*_
_*📚Ana- muslim📚*_
•
•
•
:
*_TAMBAYA_*
:
_Assalamu Alaikum, Malam a sallar Nafila mutum zai iya yimata Iqaamah ko kuwa??_
:
_*AMSA:*_
:
_Aa babu iqaamah ko kiran sallah ga sallolin Nafilah. Idan kayi alwala kawai zaka sallace su ne iya yadda zaka iya a koyarwar Sunnah, kamar misali Sallar Duhaa, Nafilar bayan azahar ko kuma sallar sulusin dare na karshe, ko kuma kowane irin lokaci, amma banda lokacin da aka hana yin sallah. Duk wadannan sallolin zaka yisu ne babu kiran sallah ko iqaamah agaresu._
_Ba'a ruwaito cewa idan _*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)*_ ya miqe yin sallar nafilah yana yin kiran sallah ko iqaamah ba. Kiran sallah da iqaamah ana yinsu ne ga sallar farillah kadai. Amma sallar Tarawihi, wutiri da sauran nafiloli ba'a yi musu iqaamah ko kiran sallah, kamar yadda malamai suka fada, kuma shine sunnar _*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)*_ da hanyar khulafa'ur rashideen.
_*(Fataawa Samaahat Al-Shaykh Abdallah Ibn Humayd, shafi na 114).*_
.
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©✍🏽 Sadeeq Ñagogo{βluñgu}*_
.
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
*--------------------------*
*_•Ga mai sha'awar shiga Zauren 📚Ana -muslim_*📚
_*ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_
_*08093347777*_
_*08085777555*_
〰〰〰〰〰〰〰〰〰 _*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ ɴα ғαcєвooк ѕαι α lαtsα ɴαɴ*_ ⬇
https://www.facebook.com/Ana-Muslim-Group-156263338266984/