SHAWARWARI GA MATAR DA MIJINTA KE NEMAN MATA A SOCIAL MEDIA :



SHAWARWARI GA MATAR DA MIJINTA KE NEMAN MATA A SOCIAL MEDIA :

TAMBAYA TA 2988
********************
Assalamu alaikum,malam dapatan kuna lafiya ya iyali,dan Allah malam addu'a nakeso a taimaka man da ita ta hadin kan iyali saboda duba d yanayin da muke ciki a yanzu kana zaune lafiya da mai gidanka d yaranka a lokacin d zai kara aure wata tayi abinda zai rabaka da mijinka da yaranka baki daya Dan Allah a taimaka Kuma wasu mazajen sukan rinka kule kelen "yanmata musamman a social media har takai ana yin abunda bai dace bah Kuma ba aurensu zaeyi bah Sam baida lokacin iyalinsa a taimaka mana da addu'a da shawarwari, Nagode,Allah ya qara qaunar SAYYADINA RASULULLAHI SALALLAHU ALAIHI WASALLAM.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Tabbas da yawa daga cikin mazaje basu fahimci irin Qunar zuciyar da matayensu ke fuskanta bane alokacin da suka Qi basu lokacinsu, kuma ba wai saboda sunyi musu wani laifi ba, kuma ba don saboda wani muhimmin aikin da ya dauke hankalinsu ba, sai don saboda yin chatting da 'Yan mata a facebook ko whatsapp. 

Allah Madaukakin Sarki ya umurci mazaje cewa wajibi ne su rike matayensu bisa amana kuma su kyautata mu'amalarsu dasu. Hakanan kuma ya fa'da acikin Suratul Baqarah cewa "SU MA (MATAYEN AURE) SUNA DA HAKKI (AKAN MAZAJENSU) KWATANKWACIN IRIN HAQQIN DAJE KANSU NA MAZAJENSU".

Wato kamar yadda ya zama wajibi akan mace ta girmama mijinta kuma ta kyautata masa, ta bashi dukkan lokacinta, to shima wajibi ne ya girmamata amatsayinta na mutum, ya girmamata amatsayinta na musulma muminah, sannan ya girmamata amatsayinta na amanar Allah dake karkashin kulawarsa, kuma ya bata dukkan lokacinsa aduk lokacin da yake gida, sannan ya rika kiyaye abinda zai kawo zargi da zubewar mutunci tsakaninsa da iyalinsa.. 

Shawarar da zan baki awannan yanayin shine kiyi iyakar bakin kokarinki wajen daukar hankalinsa ta hanyar tsafta da Qayatar da Girkinki, jikinki da dakinki da shimfidarki, da gidan ma baki daya. 

Sannan ki lalubo duk wani laifin da kika san baya so, ki gyara, ki kyautata duk wata mu'amala tsakaninki dashi, sannan kema ki rika tura masa kalaman soyayya ta hanyar text koda yana wajen aiki ko kasuwarsa... 

Idan ya dawo gida kuma ki tarairayi abinki, ki nuna masa tamkar baki da wani uzuri aduniyar nan bayan ibadunki na farilla sai kula da mijinki. Mafiya yawan matan hausa/fulani kamar wani irin girman kai ke damunsu. Suna ganin tamkar sunfi karfin su bawa namiji hakuri idan sunyi masa laifi, kuma suna jin nauyin su rika tarairayarsa. 

Ba wani abu bane yake dauke hankalin wasu mazajen auren daga kan matayensu, har su koma yin chatting da 'yan mata fache rashin samun tausasan kalamai daga matansu na aure, da rashin jituwa, da rashin saurin warware matsalolin gida ta hanyar laluma da sulhu. 

Daga karshe kuma ina baki shawarar ki Qara hakuri da juriya da kuma mayar da hankali wajen kyautata zance da mu'amala da maigidanki, sannan ki yawaita kula da karatun Alqur'ani da nafilfilin dare, da zikirin Allah ako yaushe. 

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10/11/1443 09/06/2022).
Post a Comment (0)