ANA YIN WUTIRI NE A KARSHEN DARE!!
*Tambaya*
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam menene hukuncin yin wuturi a lokacin taraweeh bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare?
*Amsa*
Wa'alaikum assalam,
in har mutum ya san zai yi wata sallar bayan tarawihi, to abin da yake dai dai shi ne ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare saboda hadisin da Bukari da Muslim suka rawaito cewa: Annabi (S.A.W) yana barin wutirin sa in ya yi sallar dare zuwa lokacin sahur, da kuma hadisin da Annabin yake cewa: Ku sanya wutiri sallarku ta karshe da daddare"
Bukari ne ya rawaito da Muslim.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU ZAREWA
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a
FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248