HUKUNCIN WANDA KE LEQEN TSARAICIN MUTANE :
TAMBAYA TA 2975
********************
Assalam alaykum malam tambaya ta shine menene hukuncin wanda yake leqa mutane (musamman ma 'yan mata) yayin da suka shiga bayan gida domin wanka ko kama ruwa, Nagode
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Babu shakka wannan haramun ne. Kuma duk wanda ya aikata haka tabbas ya cika azzalumi kuma fasiqi ta hanyoyi kamar haka :
1 Yin haka, leken tsaraicin jama'a, Qetare iyakokin Allah ne kuma Allah yace :
*"Wanda ya sa'ba wa Allah da Manzonsa kuma ya Qetare iyakokinsa, Zamu shigar dashi cikin wata wuta wacce zai dawwama acikinta, kuma azama mai wulakantarwa ta tabbata gareshi"*
Awani wajen kuma Allah yace *"Wanda ya qetare iyakokin Allah, hakika ya zalunci kansa".*
2. Yin haka yana daga keta alfarmar musulmi da kuma mutuncinsa. Gashi kuma Manzon Allah ﷺ yace : "Dukkan musulmi akan musulmi, haramun jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa.
3. Wannan laifin ya shafi kallon al'aura da tsiraicin mutane. Kuma Imamuz Zahaby acikin kitabul Kaba'ir ya kawo hadisin dake nuna ALLAH YA TSINE WA MAI KALLO DA WANDA AKE KALLON (Wato Allah ya tsine wa mai kallon tsaraici, da kuma wanda ke bayyanar da tsaraicinsa domin arika kallo).
To kaga anan su wadanda ake kallo din, ba da son ransu ake kallon nasu ba. Hasali ma basu bayyanar da tsaraicin ba. Don haka tsinuwar ta tattaru ne akan wannan dake kallon nasu aboye.
4. Leqen tsaraicin Muminai chutarwa ce garesu kuma Allah yace : *"WADANNAN DAKE CHUTAR DA MUMINAI MAZA DA MUMINAI MATA SANNAN BASU TUBA BA, TO AZABAR JAHANNAMA TA TABBATA GARESU, KUMA AZABAR QUNA TA TABBATA GARESU".
Amma idan ya zamanto akwai makobtaka atsakaninsu, to anan ne laifin kuma yafi girma domin Manzon Allah ﷺ yace :
"Duk wanda Makobcinsa bai tsira daga sharrinsa ba, bazai samu shiga Aljannah ba".
(IMAMU MUSLIM NE YA RUWAITOSHI).
Sannan daga karshe idan an kama irin Wadannan mutane wajibi ne akaisu ga hukuma madi kusa domin daukar matakin da ya dace akansu.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (23/05/2022 22/10/1443).