LFIFITA TSAKANIN KISHIYOYI HARAMUN NE !!!
*Tambaya*
Assalamu Alaikum.
Malam na kasance inna kyautata Ma mijina iya gwargwadona, to amma matsalan ba ni kade bace sai yakasan ce nima yana mun duk wani Abu najin dadi da kyautatawa fiye da kishiyar tawa wani Lokacimma baya Boyewa to shin malam bama Shiga hakkinta.
Menene hukuncin haka. Nagode
*Amsa*
Wa'alaikum assalam Ya wajaba ayi adalci a lamura na zahiri (kamar abinci, tufa) tsakanin kishiyoyi, Annabi ï·º yana cewa: “Duk Wanda yake da mata biyu, amma bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar alkiyama sahensa daya a shagide”.
Ya halatta in kana da mata guda biyu ka fi son daya daga ciki, ka fi jin dadin saduwa da ita, ka fi dadewa a dakinta, Annabi ï·º ya fi son nana Aisha akan duka matansa tara da ya mutu ya bari, kuma matansa da sahabbansa sun san hakan, kamar yadda ya tabbata a sahihul Bukhari.
Allah ne mafi sani.
12/08/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a
FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248