KA YIWA KANKA HISABI KAFIN KA KWANTA BARCI
Sayyadina Umar R.A yana cewa:
"kuyiwa kanku hisabi kafin ayi maku hisabi,kuriqa auna aiyukan kafin a auna maku....."
ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa:
"Mai yafi alkhairi fiye da mutum yayi amfani awa guda lokacin kwanciya barcinsa yayiwa kansa Hisabi akan abinda yayi hasara na awowin yininsa da daransa,sannan ya sake jaddada TubaIngantacce tsakaninka da ubangijinka,sai mutum yayi barci cikin tuba mai kyau tare da azamar bazai sake komawa ba zuwa ga wannan zunubinba anan gaba ba.idan ya tashi cikin nishadi na niyyar kyautata aiyukan wannan yinin da yawayi gari..........."
@ﺍﻟﻤﺮﺟﻊ / ﺍﻟﺮﻭﺡ ﺹ : 79
Hakan ya zama Sunnar magabata suna yiwa kansu hisabi lokacin kwanciya barin su,sai hakan ya taimaka masu wajan takaita aiyukan saboda da tuba daga laifuka da komawa zuwa ga Allah da yawaita aiyukan dha'a.
Yakai Dan uwana mai albarka saunawa muka taba yiwa kanmu haka,idan munayi sai mu kara himma wajan cigaba, idan kuma baka tabayi ba yakamat ka dauri niyyar haka cikin wannan dare,domin Mutuwa bata da lokacin.
Allah ka bamu ikon yin hakan amin.