JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 15
BANU ISRA'LA DA YAHUDANCI
Duk wani dan banu Isra'ila za ka iske yana hada kansa ne da saqon da Musa AS ya zo da shi, wanda shi suke kira da Yahudanci a yau, duk da cewa akwai manzanni da yawa da suka shiga tsakankanin Annabi Musa da mu, kuma duk wadannan manzannin su din dai aka tura musu su, zan so mu riqa tuna wa junanmu cewa Annabi Isa AS shi ne qarshen manzo da aka tura wa banu Isra'ila, amma yadda ba su yi imani da Annabi Muhammad SAW ba haka ba su yi imani da Annabi Isa AS ba, yadda ba su damu da jinin duk wani musulmi ba haka ba su damu da jinin wani kirista ba, bare ma sun bar wa sauran al'umma ne addinin kiristancin su ba ruwansu, gashi kuma su kadai aka aika musu da Annabi Isa AS din.
.
Yanzu mu kalli yadda dabi'unsu yake a Qur'ani bayan Sulaiman AS:-
1) Mutane ne masu son tara dukiya, kuma ba su damu ko ta wace hanya za su samu ba {قَالَ الَّذِينَ يُرِيدُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا يَلَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَا أُوتِيَ قَارُونُ إِنَّهُ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍ} (Wadanda suke son rayuwar duniya suke cewa: Ina ma da muna da kwatankwacin abinda Qaruna yake da shi ai ya yi babbar sa'a) Qasas 79. Ko za ku kashe kawunanku wannan a wurinsu ba wata matsala ba ce.
.
Bayan Annabi Sulaiman AS ba a nuna wani annabi cikin 'ya'yansa da ya gaje shi a mulki ba to bare kuma ragamar manzanci, sai lamuransu suka koma hannun sarakuna zalla, sha'anin mulki ya sami gindin zama, yanzu ba maganar ibada ko manzanci ake yi ba, mulkin ne kawai, kun ga zuwa yanzu ma mun kai yadda ake cewa jagoranci daban addini daban, ba ruwan al'umma da sai an bauta wa Allah amma kar a tabi jagoranci, haka banu Isra'ila suka manta da asalinsu tun Isra'ilan kansa wato Ya'kub AS wanda tsatsonsa ake kira banu Isra'ilan.
.
Sai al'ummar ta juyo wa mulki zalla aka yi ta rige-rige a kanta ana digirgire da rayukan jama'a ko kuma sarakunan, ina son na ce in sun kashe annabawa don ba sa son wani abu ya zama musu qalu-bale to ba za su bar junansu a kan mulki ba, a qissoshin da aka samu cikin Attauransu a shekaru 300 an yi sarakuna 22 inda za a qiyasta kowani sarki daya ya yi kwatankwacin shekara 14 kenan saboda yawan kisar gillar da aka yi ta yi wa sarakunan a tsakankaninsu, ba su kadai ba har da malamansu da masu bautansu.
.
Abinda zai ba ka mamaki galibin sarakunan matasa ne, an riqa samun kashe-kashe da yara kan yi wa mahaifansu don samun damar isa ga mulki, wannan har yanzu yana faruwa a tsakaninsu da sauran qasashen da suke ma'amalla da su, to sai dai ko wannan lokacin akan riqa samun annabawa da mutanen kirkin da za su kirawo su zuwa ga shiriya, kuma dalilin dake sanyawa kenan su kashe su, tare da sakankacewar tabbas annabawan ne, sai aka riqa samun masanansu suna share rubutun littafan Allah suna sanya wanda zai yi daidai da abinda zuciyoyinsu suke so.
.
2) Tabbatuwar cewa sun bauta wa wanin Allah, sun yi shirka da shi, Allah SW yake cewa {قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُمْ بِشَرٍّ مِنْ ذَلِكَ مَثُوبَةً عِنْدَ اللَّهِ مَنْ لَعَنَهُ اللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ الْقِرَدَةَ وَالْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ الطَّاغُوتَ أُولَئِكَ شَرٌّ مَكَانًا وَأَضَلُّ عَنْ سَوَاءِ السَّبِيلِ} (Bana ba ka labarin wadanda suka fi munin sakamako wurin Allah ba kamar wanda Allah ya tsine masa, ya yi fushi da shi ya sanya birrai da aladu a tsakaninsu, ya bauta wa dagutai, wadannan su ne mafi sharrin matsayi mafi bacewa daga hanya madaidaiciya) Ma'ida60. A qarshe sun ce Isa AS ma Allah ne suka bar wa duniya ta bauta masa su suka qi.
.
3) Warware alqawari, boye maganar Allah da canjata, Allah SW ya ce {فَبِمَا نَقْضِهِمْ مِيثَاقَهُمْ لَعَنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَنْ مَوَاضِعِهِ وَنَسُوا حَظًّا مِمَّا ذُكِّرُوا بِهِ} (A dalilin warware alqawarinsu muka tsine musu, muka sanya zuciyarsu ta bushe suna jirkita zance sabanin yadda yake suka mance saqon da aka tunatar musu) Ma'ida13.
4) Bauta wa aljanu da shedanu da koyon tsafi gami da alkatawa Allah SW ya ce:- {وَاتَّبَعُوا مَا تَتْلُو الشَّيَاطِينُ عَلَى مُلْكِ سُلَيْمَانَ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَكِنَّ الشَّيَاطِينَ كَفَرُوا يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ} (Suka bi abinda shedanu suka riqa karantawa a kan mulkin Suleiman, Sulaiman bai kafurta ba shedanun ne suka kafurta, suna koya wa mutane sihiri) Baqara102.
.
5) Karbar rashawa da cin dukiyar mutane, Allah SW ya ce {وَأَخَذِهِمُ الرِّبَا وَقَدْ نُهُوا عَنْهُ وَأَكْلِهِمْ أَمْوَالَ النَّاسِ بِالْبَاطِلِ وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ مِنْهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا} (Da karbar riba alhali an hana su, da cin dukiyar mutane bisa zalinci, mun tanadar wa kafurai a cikinsu azaba mai radadi) Nisa'161.
6) Sun dena da'awa, ba umurni ba hani Allah SW yake cewa:- {كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَنْ مُنْكَرٍ فَعَلُوهُ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ} (Ba sa hana juna aikata wani mummunan aiki da suka riqa yi, tir da abindaa suka riqa aikatawa) Ma'ida79
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248