JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 14
QASAR BANU ISRA'ILA
Ainihin wurin na Kan'aniyawa ne, in za mu tuna mun san lokacin da tarihi ya dauko mana hijirar Ibrahim AS daga qasar Babil wato Iraqi zuwa Jordan, da wucewarsa suwa Masar, da dawowarsa zuwa qasar Kan'an wato Palestine kenan a yau lokacin Kan'aniyawa na wurin, shi ya sa lokacin da Yusuf AS ya gayyato babansa da sauran 'yan uwansa zuwa Masar ba a yi maganar wani dangi da suka bari ba, ko lokacin da suka yi niyyar komawa Kan'an neman inda wurin yake ne suke yi, kenan ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa tsakaninsu da wurin, wannan qabilar ita ake ta fama da ita tun bayan wafatin Musa AS, su ne suke kiran kansu Yahudawa, su suka riqa kashe manzannin Allan da kansu, to ta ya wani addini ma zai dame su?
.
Ko a zamanin Musa AS cewa suke yi "Roqa mana Ubangijinka" ba sa sanya kawunansu kwata-kwata, kenan qabilar ce ta hada galibinsu da Annabi Musa AS ba wai addinin da bautar Allah SW ba, shi ya sa duk wani manzo ko annabi in aka turo shi wajensu yake dandana kudarsa a hannunsu, wannan in ma sun bar shi da rai kenan, daga zamanin Musa AS zuwa Dauda AS sun kashe annabawa da yawa wadanda aka turo su wajensu, kisar ba ta tsaya anan ba, karatu na gaba in da rai za mu gani, a yau dai musulmai da kiristoci sun yarda da annabcin Dauda AS banda yahudawa, duk girmamawar da suke masa ba su yarda da annabcinsa ba.
.
A zamanin Musa AS yake ce musu يَا قَوْمِ لِمَ تُؤْذُونَنِي} وَقَدْ تَعْلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ فَلَمَّا زَاغُوا أَزَاغَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ} (Jama'ata don me kuke cutar da ni bayan kun san cewa ni manzon Allah ne gare ku, yayin da suka juya baya Allah ya juya zuciyarsu, Allah ba ya shiryar da azzalumai) Saffi5. Har yau ba sa nadama a kan abubuwan da suke aikatawa, kisa da daukar kowa ba komai ba ne, satar dukiyar jama'a da raba kan mutane shi ne kadai a gabansu, sukan shiga addinin mutane su yi musu rubuce-rubuce su raba kawunansu su kautar da su daga addinin don dai a zama daya.
.
A bayyane yake Allah SW yana ce لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن} بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَوْا وَكَانُوا يَعْتَدُونَ} (An tsine wa kafuran cikin banu Isra'ila ta harshen Dauda da Isa dan Maryam saboda sabawarsu da wuce gona da iri da suka riqa yi)Ma'ida78. Sun saba wa Dauda AS shi ne farkon sarki daga cikinsu, sun saba wa Isa AS shi ne qarshen annabin da aka turo a cikinsu, a tsakiya kuma ga annabawanan da dama da aka yi ta turo musu ba abinda ya bambanta su da sauran.
.
SULEIMAN AS
Daya ne daga cikin manzannin da Allah SW ya aika wa banu Isra'ila, tsarin mulkinsu ya koma na gado, don kuwa rantsattsen sarki a cikinsu Dauda AS ne, bayansa sai dansa na cikinsa wato Suleiman AS, tarihi ya nuna cewa shi Dauda AS ya tabbatar musu da mulkin Qudus da cewa qasarsu ce, sai dai iyakarsu kenan cikin Qudus din har bayan rasuwarsa, amma da Suleiman AS ya zo shi ne ya fadada qasar ta shafi wasu qauyukan dake zagaye da Qudus din, sai dai duk da haka daular tasa ba ta gama da Palastinawa duka ba, ta gabashi dai sun kai kogin Jordan, ta yammaci kuma sun hadu da teku illa iyaka, in kuma da wani qari to Allah ne masani.
.
Annabi Suleiman AS ya shimfida mulkin da ba wanda ya yi irinsa a cikin mutane, koda yake dama ya roqi Allah ne ya ce { اغْفِرْ لِي وَهَبْ لِي مُلْكًا لَا يَنْبَغِي لِأَحَدٍ مِنْ بَعْدِي إِنَّكَ أَنْتَ الْوَهَّابُ} (Ka gafarta min, ka ba ni mulkin da ba wanda zai sake samunsa a bayana lallai kai mai yawan baiwa ne) Dad35. Ba wai fadin qasa ne ba, irin mulkin da Annabi Suleiman ya yi ba a taba samun sarkin da ya yi shi ba har yanzu, don mutum da aljan suna qarqashinsa ne hatta dabbobi, Qur'ani ya kawo mana tattaunawar wasu dabbobi ko dai da shi ko kuma ya ji, kamar dai hudhud ko tururuwa da sauransu.
.
Iska ma tana kadawa da umurninsa, kamar yadda Allah SW ya fadi { فَسَخَّرْنَا لَهُ الرِّيحَ تَجْرِي بِأَمْرِهِ رُخَاءً حَيْثُ أَصَابَ} (Muka hore masa iska wace take kadawa a hankali da umurninsa zuwa inda yake so) ga shedanu magina dake gina masa duk abinda yake so da 'yan-ruwa dake ciro masa kayayyakin alatu da sauran abubuwan ruwa, shedanu na hannunsa ne suna yi masa aiki, akwai wasu abubuwa na baiwa wadanda Allah SW bai ba kowa ba sai shi.
.
Tarihi ya nuna cewa shi ne ya fara gina masallacin Baitul Maqdis, kuma an gina masallacin ne da kayan qawa sosai, ba ma irin kayan da muka saba gini da shi ba, wannan ba abin mamaki ba ne don maginan ba mutane ba ne, kayan ginin za su iya samo shi a ko'ina su kuma gina shi yadda suke iyawa, wannan na daya daga cikin abinda ya janyo hankulan sarakan duniya zuwa yaqar masallacin don su kwashe kayan dake cikinsa na qawa, koda yake wasu malaman muslunci na musanta hakan don kauce wa cewa masallacin na banu Isra'ila ne, koya abin yake masallacin dai na muslunci ne.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248