JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 026

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 026



YAQIN KHAIBAR
In mai karatu ya lura da kyau duk yaqoqin da aka yi da Yahudawa a yankin Madina, masamman wadanda aka kora za ka ji sun yi tafiyarsu ne zuwa Khaibar bayan sun rabu da Madinar, domin ita din a Saudiya take Arewa da Madinar, dama manya-manyan qalu-balen da muslunci yake fama da su Quraishawa ne a Madina da Yahudawan dake ciki, to bayan an yi yaqin taron dangi (Wato Ahzab) sai kan Yahudawan da Quraishawan Makka ya rabu, wannan yaqin ya zama na qarshe wanda bayansa Quraishawan ba su sake yin gangami don zuwa yaqar musulmai a Madinan ba, gamawa da Yahudawan banu Quraiza kuma sai ya zamanto su ne matattarar Yahudawa ta qarshe da ta rage a jikin Madina.
.
Da wannan za a iya cewa muslunci ya yi fatali kenan da duk wani gungu na abokan gaba wanda zai iya abka masa kai tsaye, sai dai kuma yahudawan banu Qainuqa da na banu Nadir da ma mata da qananan yara na banu Quraiza wasunsu sun nufi Sham can ainihin qasarsu, amma fa akwai sauran burbushinsu da suka walkata akalarsu zuwa Khaibar inda adadi mai dama na Yahudawa yake can, ma'ana tsuguno kenan bai qare ba, in muslunci yana son ya zauna lafiya dole sai ya tarwatsa wannan tsaunukan na Yahudawa dake kwance a Khaibar.
.
DALILIN YAQIN
Bayan kammala yaqin Khandaq wanda ake wa laqabi da Ahzab wato yaqin taron dangi sai Annabi SAW ya qulla yarjejeniyar sulhu tare da Quraishawa, wannan yarjejeniyar dayawan mutane ba su fahimce ta ba, amma jagoran muslunci a lokacin wato ma'aikin Allah SAW ya fahimce ta sosai, shi ya sa ya yi aiki da wannan damar don ya yaqi Yahudawan ba tare da Larabawan Makka sun saka hannu ba, a daya hannun kuma akwai Larabawan Najad da ma wasu wadanda duk sun saka hannu a yaqin taron dangin, in aka cire hannun Makkawa to kashinsu ya bushe.
.
Yanzu me ya kawo yaqar Khaibar da Annabi SAW ya yi? 
1) Matuqar Yahudawan ba su daina yi wa musulmai bi-ta-da-qulli ba to bai dace ba a daga musu qafa, dole a yaqe su kamar yadda suka sa muslunci a gaba, sai hukumar ta muslunci ta fita daga matsayinta na kare kai ta koma kai farmaki ga duk wata hukumar da ba ta shiga taitayinta ba, wannan zai ba muslunci qarfin da zai tsaya da qafarsa a doron qasa ya kuma jagoranci al'umma, idan muka ce muslunci to muna maganar daular muslunci ne wace helkwatanta ke Madina garin manzo, ba wata qabila ta Larabawa ko ta wasu da za sake gangancin abka wa musulmi a Madina.
.
2) Asalin yaqin da aka yi na taron dangi Khaibar ce ummulhaba'isin shirya shi, ita ta gayyato Larabawan Gadafan a kan dabinon yankinsu na tsawon shekara da za ta yi ta ciyar da su da shi, Larabawan suka yarda aka kafa runduna ta mayaqa dubu shida don kawar da muslunci a bayan qasa, tunda suka fito baro-baro suka nuna musluncin suke yaqa to dole musluncin ya ja layi, ko ya batar da su ko su su batar da shi ta wurin ci gaba da hada shi fada da sauran Larabawa suna sayar wa da duk bamgarorin makamai suna kwashe kudin qasa suna mai da mutane bayi, muslunci kullun a sama yake ba a hawansa.
.
MANUFOFIN YAQIN
1) Yahudawan Khaibar suna Arewacin Madina ne, sharrinsu ga musulmai kuma ba boyayye ba ne dole a tayar da su don a sha iska, masamman bayan tabbatuwar sanya hannunsu a yaqar daular muslunci da suka yi, da qoqarin ba da damar yadda za a abka wa musulman.
2) Ba wa musulmai damar da za su mayar da Madina ta zama cikakkiyar daularsu, in ma za a sami wasu yankuna to za su biye wa babban birni ne, in hakan ya samu to duk wanda yake son ya shiga muslunci ba zai yi wani haufi ko shakka ba bare tsoron abinda zai biyo baya don ya san akwai wanda zai ba shi kariya.
.
3) Ci gaba da yada addinin muslunci a qusurwoyi daban-daban na yankunan dake zagaye da Madinan, da kuma qoqarin maida addinin Allah ya zama shi ke kan sauran addinai, dama an aiko Annabi SAW don sanya musluncin ya zama shi ke jagorantar al'umma ne gaba daya, duk kuma wani yaqi da sahabban Annabi SAW suka fita to don wannan suka yi shi, shi ya sa kowa ke jinjina wa qoqarinsu tun daga mahaliccinsu har zuwa Annabinsa SAW zuwa mumminai in ba 'yan Shi'a ba, wadanda ko kadan ba sa ganin qoqarin wadannan bayin Allan.
.
4) Idan Larabawan yankin Khaibar za su yarda su shiga yaqin taron dangi a yaqi Larabawa 'yan uwansu saboda dabino to lallai wannan dabinon ba dan qarami ba ne, in muslunci zai same shi tabbas za a yaye wa musulmai da dama talaucin da suke fama da shi ko kuma rashin abinci, babu ko shakka wadannan manufofi ciki har da na tattalin arziqi manufofi ne masu amfani ga muslunci a wannan lokacin, sannan kuma in aka tashi Khaibar ina kuma Yahudawan za su sake komawa su zauna bare su juyo su sake saka muslunci a gaba?

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)