JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 21
BAYAN HIJIRA
Dawowar Annabi SAW Madina na nufin muslunci ya sami daularsa mai cin gashin kanta, shi ne ma ya sa Annabi SAW ya sa aka sami kundi wanda zai hada kan duk al'umman dake zaune a Madina, wato daga Makkawa zuwa Madinawa da Yahudawa da sauran arnan dake kewaye da garin Madinan, muslunci bai yi juyin mulki ba don dama ba wata sahihiyar hukuma mai jagoranci, ba Madina ba ko a can Makkah ma, ana qoqarin samu ne sai ga muslunci ya kunno kai, da ya tashi shirin watsuwa sai ya zayyana duk abinda ake buqata a rubuce shi ne wannan kundin.
.
Bayan ya samu sai Annabi SAW ya dubi bangaren zamantakewa, yadda ya hada kan musulmai gaba daya suka zama 'yan uwan juna, har ma suka zama tamkar jiki daya duk yadda gaba daya ta kamu to sauran jikin zai dauka sai masassara da rashin barci, ya fadi abinda zai daure tsakanin musulmai gaba dayansu na soyayya da yiwa juna adalci, ko a zuciya ka so mutum to ka bi shi ka gaya masa, ya saka wasu haqqoqi da kowani musulmi yake da shi a kan dan uwansa a halin rashin lafiya ko mutuwa.
.
Ya koyar da musulmai mahimmancin maqwabtaka da rashin cutar da maqwabci, da ba shi duk haqqoqin da kowa yake da shi a kan maqwabcinsa, ta kai ga shi kansa Annabin yana zaton ko ma maqwabci zai iya gadon maqwabcinsa, kai Annabi ya sanar da mu cewa wanda maqwancinsa bai sami amincin sharrinsa ba ba ma zai shiga aljanna ba, dangane da bangaren al'umma kuwa ya koyar da yadda mutum zai nisanci abinda zai cutar da su koda kuwa wari ne a masallaci, ko kaki da sauran ababan qi, ya hana zubar da qazanta a hanya don wani ya cutu, ya hana zama a hanyar gaba daya sai in da dalili.
.
Sai zuminci inda ya koyar da inganta shi, ya hana yanke shi, ya sanya taimako a tsakanin musulmai a duk inda suke, ya zaburar da yin sadaqa mai gudana wace ko bayan mutum ya bar duniya ladarsa za ta riske shi, ciki akwai abinda mutum ya bari don amfanin al'umma, ladar za ta riqa bin sa matuqar ana amfani da shi, ga sadaka da zakka, sai taimakon marasa qarfi masamman ciyarwa, ko wani laifi mutum ya yi in ba zai iya warwarewa da ibada ba to ciyarwa za ta iya taimaka masa a qarshe, sai ya koyar da yadda za a yi ta'amuli da wadanda ba musulmai ba don dai a zauna lafiya.
.
Akwai wasu dokoki da qa'idoji da aka gindaya yadda musulmi ba zai shiga haqqin dan uwansa musulmi ba, in kuma ya shiga din ga hukuncin da aka tanadar don hakan ba tare da bambancewa ba, Annabi SAW ya ce ko Fatima diyarsa ce ta yi sata zai sa a yanke hannunta, tun dauri dama muslunci ya kawar da bambanci a tsakanin musulmai da cewa ba wanda ya fi wani sai dai a tsoron Allah, wannan kuwa tsanin mutum ne da Ubangijinsa, nan take ya kawar da bambanci, wariya, qabilanci da son kai, ya shimfida adalci a kan komai.
.
Wannan tarbiyyar sahabban Annabi SAW suka samu sai suka so junansu gaba daya suka iya kafa daula mai zaman kanta a dan lokaci qanqani, don dukansu suna jin cewa jiki daya ne garesu qarqashin jagorancin mutum guda a addinance, mutumin Madina bai jin cewa qasar tasa ce, haka mutumin Makkah bai raya cewa shugaban ai dan qabilansa ne, ga wahayi na saita mutane zuwa ga abinda Allah ke so da nisantar wanda ba ya so, su ma Yahudawan dake zaune da musulmai suna da sakankancewar cewa ba za a cutar da su ba.
.
Da haka sai matsalolin cikin gida duk suka yaye aka fara tunanin yadda za a fuskanci matsalolin waje, masamman Makkawa da suka musguna wa musulmai suka qwace dukiyoyinsu ba tare da dalili ba, yanzu ga muslman sun dawo Madina, sun qara wa mutanen wurin nauyi, dole su fara tunanin yadda za a yi su karbo haqqoqinsu don ci gaba da rayuwa a Madina kamar kowa, dalilin kawo tsare-tsaren da za su daga musluncin sama kenan, in wani zai shiga to zai iya shigowa ba tare da wani tsoro a kansa ko a rayuwarsa ba, tunda Madina ta zama qasar musulmai kuma yanzu akwai hukuma sai:-
.
1) Annabi SAW ya samar da masu leqen asiri na masamman, wadannan ne suka fara gano cewa tawagar Quraishawa ta tafi Sham kasuwanci kamar yadda ta saba, jagoranta shi ne Abu-Sufyan, shi ma ya ji a jikinsa kuma ya gano cewa akwai yuwuwar kwanton bauna a hanya sai ya tura wa Quraishawa da saqo don su zo su qwaci kayansu, wannan shi ne babban dalilin yaqin Badar, akwai wasu yaqoqi da dama da musulmai suka ci nasara qarqashin tura wadannan masu binciken, don su suke gano matsaloli da haqiqanin muslunci kamar yadda suke, sai kuma su yi nasiha don a yi gaggawar daukar mataki har sai an ci nasara.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248