JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 20
KUNDIN TSARIN MULKI
Koda a ce wasu daulolin da suka ci gaba suna da wani kundi na tsarin mulki za ka taras yana kare martabar masarauta ne kawai da zaben shugabanni, in muslunci zai kwaikwayi wadannan qasashen tabbas akwai buqatar a sami kwafi a karanta don bibiya ko samun wani sabon daftarin da zai yi daidai da musluncin ko musulman gaba daya, amma sananne ne cewa wannan sabon daftarin an yi shi ne da umurnin Annabi SAW, kuma ansan rayuwarsa gaba daya, ta fara ne daga qauyen qayau inda aka reneshi, aikinsa a lokacin kiwo ne.
.
Fitarsa zuwa kasuwanci Sham amanarsa Khadija ta gani ba gwanancewarsa a fannin ba, kuma an ja kunnen magabatansa tun daga lokacin kan cewa su daina barinsa yana yawo, wannan bai isa a ce har ya ga wata wayewa daga wani wuri ya dauko don ya gina daularsa da ita ba, abin nufi wani haske ne kawai daga Allah SW ya ni'imta manzonsa da shi wurin kawo wannan kundi, wanda har wadanda ba musulmai ba ma sun yi bincike a cikinsa sun gano wasu tsare-tsare na masamman wadanda za a iya aiki da su a wasu daulolin wadanda ba ma na muslunci ba matuqar ana son zaman lafiya.
.
Constance George yake cewa "Wannan kundin na muslunci ya qunshi dokoki 52 dukansu daga manzon Allah ne, guda 25 sun shafi musulmai ne kadai, 27 kuma suna da alaqa tsakanin musulmai da sauran wasu addinai can daban masamman Yahudawa da masu bautar gumaka, an tsara kundin yadda zai ba wadanda ba musulmai ba damar rayuwa da su a cikin 'yanci, kuma za su iya gudanar da addininsu gwargwadon yadda suke so, sai dai kuma a duk lokacin da za a yaqi Madina dole ne kowa ya zo qarfi da qarfe, harshe da harsashi don a hadu a kare Madinar" (Al-shikh, Mamdouh, Madkhal ila Saqafati Qabulil Akhar, 2018).
.
Saba wa wannan kundin shi ya jawo aka yaqi Yahudawan Madina bayan yaqin Ahzab, don suna qarqashinsa, ga shi a taqaice:-
I) Musulman cikin Madina su da Makkawa kansu guda ne a kan komai na addini, sabanin wadanda ba musulmai ba.
II) Muhajiran Makka da suka zo Madina, da sauran dangogin cikin Madinan kamar su: Banu Auf, banu Sa'ida, banul Harith, banu Jusham, banun Najjar, banu Amr, banun Nabit, banul Aus, kowace qabila cikinsu tananan a matsuguninta a cikin Madina, 'ya'yanta za su riqa taimakon junansu a komai na abinda ya shafe su su kadai, in an kama wani ko mai rauni a cikinsu su hadu su karbo shi cikin adalci gwargwadon yadda shari'a ta tanadar.
.
III) Muminai gaba dayansu in wani abu na qaruwa ya samu kar su bar shi a tsakaninsu, su bayar da shi gwargwadon iko wajen taimakawa ko qwatar wani, kar wani mumini ya je ya yi mu'amalla da bawan wani ba tare da ya tuntubi mai shi ba.
IV) Kar wani musulmi ya kashe dan uwansa musulmi a kan kafiri, ko ya taimaki kafirin a kansa, duk matsayin musulman daya ne, qaramin cikinsu zai iya tsaya wa wani.
V) Duk wanda ya bi mu cikin Yahudawa ya zama kamar kowa yana da kwatankwacin haqqoqi.
.
VI) Wata qabila cikin muslunci ba za ta je ta yi sulhu da wasu ba sai da yardar sauran qabilun musulmai da amincewarsu.
VII) Wani mayaqi da aka gwabza da shi ya bambanta da wanda ya muslunta a bayansa bai yi gwagwarmayarsa ba.
VIII) Sauran fifiko kan kasance ne tsakanin muminai gwargwadon qoqarin mutum ta wurin ba da kansa da dukiyarsa.
IX) Muminai za su hadu gaba daya a kan tsoron Allah da bin tafarki madaidaici.
X) Kada wani kafiri ya ba wa kafiran Quraishawa Mafaka ko dukiyarsu, haka kar wani mumini ya hana dan uwansa mumini isa ga dukiyar kafiran Quraishawa.
.
XI) Duk wanda ya kashe mumini za a kashe shi, sai in masu jinin sun yafe, duk musulmai za su game masa kai ba wanda zai goyi bayansa.
XII) Bai halasta ba ga wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma amince da abinda ke cikin kundin mulkin da aka yi ya ba da kariya ga wani mazinaci saboda barnarsa da ya yi, wanda ya yi haka tsinuwar Allah da fushinsa za su tabbata gare shi, ba za a sake karbar shedarsa ba ba kuma za a amince da shi ba.
XIII) Duk wani sabani kuma da za ku yi to a dawo da shi ga Allah da manzonsa.
.
XIV) In dai mutanen Madina za su shiga yaqi to Yahudawan dake zaune a can su ma za su sa hannu wajen taimakon cin nasarar yaqin da abinda ke hannunsu.
XV) Yahudawan banun Najjar, banul Harith, banu Sa'ida, banu Jusham, banu Sa'alaba, banu Shatiba duk kamar banu Auf ne; suna da kwatankwacin abinda ke kan musulmai har da bayinsu, sai dai kowa da addininsa, wanda ya yi zalunci shi ya halakar da kansa da iyalinsa saboda barnar ya yi.
XVI) Biyayya da natsuwa ake so ga mabiya ba barna da sabo ba.
.
XVII) Duk wani Bayahuden Madina ba zai bar jama'arsa ba sai da izini daga Annabi SAW.
XVIII) Ba za a hana wanda aka wa rauni ya dauki fansa ba.
XIV) Dun wanda ya je ya yi kisa ya zalunci kansa da iyalinsa in ba kisar ta jikinsa ce ba.
XV) Yahudawa da musulmai kowa da gidauniyarsa, amma akwai taimakekeniya in wani zai shiga yaqi, kuma kowa zai iya jan hankalin dan uwansa a kan gaskiya ba bata ba.
.
XVI) Za a taimaki wanda aka zalunta ne.
XVII) Madina za ta zauna cikin aminci ga duk wanda yake qarqashin wannan kundin.
XVIII) Duk wanda ya tsaya wa wani daidai yake da kowa, ba za a ci mutuncinsa ko a taba masa wani abu ba.
XIX) Duk wani rashin fahimtar juna ko jajayayya da aka samu to sai a koma ga Allah SW da manzonsa.
XX) Ba a taimaki kafuran Makkah ba ta kowace hanya, duk wanda ya tsaya musu to fa da musulmai yake yi.
XXI) Wannan kundi bai ba da wata kafa ga azzalumi ko mai saba wa shari'a ba.
XXII) Duk wanda ya bar Madina kamar wanda yake ciki ne sai wanda ya bantaro wa kansa wani abin.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248