JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 22

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 22


2) DUKAR TATTALIN QASA
Duk yaqoqin da suka faru tsakanin musulmai a Madina da Quraishawa a Makka qoqarin kare tattalin arziqin qasada ya kawo shi, domin kuwa Quraishawa suka fara qwace dukiyar musulmai a Makka, hakan ta sa suka miqe don maido da haqqoqinsu a lokacin da Quraishawa suka fito kasuwanci , domin kuwa ba su da wata hanya da za su iya isa Sham ba tare da sun wuce Madina ba, shi ya sa ma da Abu-Sufyan ya kawo musu dukiyarsu suka sha alwashin za su koma da ita su yaqi muslunci don su sami damar dauke takumkumin da musulman suka daura musu na rashin iya gudanar da kasuwancinsu kamar yadda suka saba.
.
Kenan ba musulmai suka nemi a yi yaqin ba, sun dai fito kare kansu ne daga harin Quraishawa kuma Allah SW ya ba su ikon kare yin hakan, sahabbai ne tare da Annabi SAW suka shiga yaqin, hankali ba zai taba dauka ba a ce Aliy RA shi kadai ya yaqi kusan mutum dubu daya kuma ya ci nasara a kansu, bare kuma ga nassi qarara da ya nuna wadanda suka yi yaqin, dalilan da za su sa sahabbai su fito yaqi sanannu ne, don an riga an zama daya, a shirye kowa yake ya mutu don daukakar muslunci, Allah ya ga zuciyarsu kuma ya ba su nasara, kusan duk manyan da suka riqa azabtar da su sun mace tun a wannan yaqin wato Badar.
.
To bayan yaqin ya qare buqatar Quraishawa ta qara yawa:-
1) An kashe musu manyansu suna da buqatar daukar fansa dole manyan muslunci su ma su mutu, shi ya sa aka sa ranar sake karawa.
2) Abin kunya ne a ce sun qyale musulmai su ci bulus, don dama sun ce za su shiga yaqin ne don nuna wa duniya cewa suna da qarfinsu, to ga shi an illata su, yaqi bai qare ba kenan.
3) Babban maqasudin yaqin shi ne bude hanyar kasuwancinsu na hunturu da bazara, hanyar kuma ba za ta taba buduwa ba sai an kawar da muslunci, ba su yi hakan ba su an illata su, magana ba ta qare ba kenan.
.
4) Wasu da dama an kashe makusantansu, an kame wasu a matsayin bayi, abinda ke ba su takaici kuma wadanda suka raina dinnan ne dai suka yi musu wannan abinda suke kira aika-aika, kenan akwai buqatar dawowar don su dauki fansa.
5) Matuqar Annabi SAW da sahabbansa na Madina to fa adadinsu dada qaruwa zai yi, wato yawan masu kwararowa bautar gumaka zai ragu, wannan zai daki tattalin arziqin Makka, dole a kawar da bautar muslunci a Madina, banda wadannan dalilai Makkawa ba su da wata buqata ta yaqar Madina don ba su yi ba a baya, hasali ma sun fi kowa son zaman lafiya da Madinawan ko don hanyarsu ta zuwa kasuwanci.
.
Tarihi ya nuna mana cewa Quraishawan sun yi qoqarin zagaye Madina zuwa Sham amma musulmai sun tarar da su dole suka watsar da kayan suka ranta-a-nakare, wannan ya dada jefa tsoro a zukatan duk wani Baquraishe dake zama a Makka, masamman mai gaba da muslunci, su kuma musulman tare da qarancinsu sun sami qwarin gwiwa daga Allah SW saboda qoqarinsu na daga kalmar Allah, koda aka ce musu za a dawo yaqi na biyu ba su girgiza ba don sun ga yadda yaqin farko ya gudana, na biyun ma suna sa rai da gamawa da kafuran.
.
ABIN KOYO A YAQIN FARKO NA TAHO MU GAMA
Koda yake akwai kai kora da aka yi kafin Badar amma fitaccen yaqi na farko shi ne Badir din, ya yi suna sosai kasancewarsa babban yaqi na farko kuma a cikinsa ne manyan mushrukan Makkah suka baqunci lahira, ga wasu ababan lura a yaqin:-
1) Darajar Quraishawa ta fadi warwas a idon Larabawan yankin, kowa ya san cewa arcewa suka yi a guje kuma manyansu ma sun bar su a baya.
2) An sami wani qarfi a yankin wanda ya sa sauran al'ummai suka fara tunanin yadda za su yi ma'amalla da su don kare kansu.
.
3) Daga wannan yaqin munafurci ya fara bayyana a Madina, nan ne aka gano ashe akwai masu shiri da Quraishawa a cikin Madinan, wadanda ba musluncin ne a gabansu ba ko tun farko ma ba sa marhabin da shi.
4) Yahudawan Madina sun fara nuna rashin gamsuwarsu da kasantuwar muslunci a yankin, tunda annabin ya fito ne a cikin wata qabilar ba tasu ba, shi ya sa suka fara qoqarin bayyana adawarsu baro-baro masamman Yahudawan banu Qainuqa.
.
5) Tun wannan yaqin aka shiga sabin yaqoqi na sai-baba-ta-gani tsakanin musulmai da Quraishawa, wanda ba a ga qarshensa ba kwata-kwata sai bayan Fathu-Makka.
6) Wasu qabilun dake kusa da Madina sun sami damar shiga muslunci ba tare da tsoron komai ba.
7) Muslunci ya yi qarfin da ya fara aiki da makami don kare kansa, wato dai daula ta kafu kenan da gaske a gaban wasu daulolin, akwai qalu-bale kenan na masamman.
8) Bayan yaqin Badar sahabbai sun samu wani girma na masamman, akwai yuwuwar ci gaba da samun irin wannan matsayina a sauran yaqoqi masu zuwa.


Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)