JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 19
Za ka yi mamaki idan aka ce maka banu Isra'ila ko Yahudawa sun zauna a Madina lokaci mai tsawo kafin zuwan Annabi SAW, amma in ka ga wahalar da suka sha na tsawon shekara 40 suna haqilon gano bigire mai tsarki wato Qudus, da yaqin da suka shiga tare da mugun tsoron mutuwarsu za ka gane ba abin mamaki ba ne in aka dake su suka watse kuma suka sami labarin cewa akwai annabin da zai fito a Madina su zo wurin su tare don ya fito a cikinsu su ci gaba da mulkar duniya, Allah SW dai ya daukaka su don kusan komai su ne farko, mun kuma fadi dalili, a lokacin manzanninsu ke jagorancinsu, duk kuma wani manzo daga wurin Allah SW yake amso saqonninsa, sai dai an yi rubuce-rubuce kan samuwarsu a wurin.
.
Akwai wanda ma ya ce Yahudawan suka kafa Madinar gaba daya (Margolis, Marx, Alexander, 2014 Tarikhu sha'ab yahudi p31) tarihin zuwan Yahudawa Madina ko Yathrib kamar yadda aka riqa kiransa a baya ya kasu zuwa gida biyu ko sama da haka, amma abinda suka tsayawa a kai shi ne kasuwar tarihin zuwa gida 2, na farko dai sun ce tun lokacin Musa AS ne, wasu kuma suka ce lokacin Nebuchadnezzar ne na biyu, don shi ne ya yi sanadiyyar qwace Qudus daga hannun jikokin Daud AS har sau biyu, na farko a shekara ta 597 kafin haihuwar Annabi Isa AS, na biyu a shekara ta 587 kafin haihuwarsa (As-Samhudi, Wafa'ul wafa bi akhbari daril Mustapha, 1419, bugu na farko, juzu'i na farko p128).
.
Qabilun Yahudawa da suka zauna Madina sun fi goma sai dai an fi sanin 4-5 ne saboda abubuwan da suka faru a wancan lokacin tsakaninsu da ma'aiki SAW, ga duk mai karanta tarihi zai ga cewa abinda suke yi a baya shi ne dai suka so aikatawa a wannan yankin, muna gangarowa a hankali, iya zaman da banu Isra'ila suka yi a Madina ba su qarqashi kowa cin gashin kansu suke yi (Bitrus Al-Bustani, Da'iratul ma'arif, juzu'i 11 p672) wannan dama da suka samu ta cin gashin kai ita ta saka suke ganin cewa daidai suke da kowa ko kuma duk mutanen wurin suna qarqashinsu ne, su ke da wuqa da nama, wanda yake son zama lafiya to dole ya rabe su, a cikin wannan halin ne Annabi SAW ya iso Madina.
.
Dangane da sana'a da kasuwanci kuwa dama Madina kamar zango take na fataken dake karakaina tsakanin Qasashen Sham zuwa Yaman, ga ta qasa ce mai albarka dake daukar noman dabino, zuwan Yahudawa yankin wasu qabilunsu guda biyu wato Banin Nazeer da banu Qainuqa suka yi maza suka yi halin hankaka wato maida dan wani naka ta yadda suka mamaye noma da cinikin dabinon (Philip K. Hitti, Tarikhul Arab, 2009, p153). Ba shikenan ba akwai wasu sana'o'in da suka yi fice a tsakaninsu a wannan lokacin kamar kasuwancin jauharori da zinare (Marks 2014), da sauran sana'o'in hannu kamar qirar farin qarfe da makami, wannan bayan mamaye hurdan kasuwanci da suka yi kenan, suka jefa mummunar riba a duk mu'amalar kudi (Taufiq Pro 2001, Tareekhul Arab Al-Qadeem, p188).
.
A irin wannan yanayin Muhammad SAW ya same su, amma kafinnan zai yi kyau mu san wane Muhammad SAW, Balarabe ne daga Makka cikin mutanen da suka shagalta kasuwanci da kiwo, wani ilimin karatu da rubutu ya yi Gabas su kuma sun yi Yamma, ba su da wata wayewa ta manyan daulolin duniya na wannan lokacin, shi ma da aka haifo shi haka yake, a maimakon ya tafi cikin manyan daulolinnan don qaro karatu da wayewa sai aka dauki rainonsa a qauyen qayau inda ya ci gaba da kiwon tumaki har ya taso, zuwa wani dan wannan lokacin amanarsa da gaskiyarsa suka fara bayyana:-
1) Abu na farko da ya fara ba wa mutane al'ajabi da shi shi ne yadda duk Makkah aka yarda da amanarsa har yana iya raba babbar matsala kamar saka Hajarul-aswad a cikin Qa'aba.
.
2) Aurensa da Khadija wace take babbar mace, ta ma qi manyan mutane da suka fito nemanta, masu kudi, dangane da komai, ga ta daga babban gida, ga ilimi har tana karanta Attaura, kuma ga dukiya, amma ta aure shi.
3) Zuwa da wani saqo wanda ya gagari kowa, duk in mutum ya yi niyyar cutar da shi sai ya koma mabiyinsa, wasu da yawa sun rasa uwayensu, 'ya'yansu, abokan zamansu da masoyansu, saboda sun bi shi.
4) Samun alaqa da wata qasa ta qetare a karon farko a yankin, yadda ya iya tura mabiyansa zuwa Habasha, kuma suka sami karbuwa ta girmamawa, wanda a baya babu tsari na shugabanci a yankin har da za a sami alaqa da wata daular ta kai tsaye.
.
5) Fara kafa hukuma mai zaman kanta a yankin, wace take gudanar da al'amuranta cikin sirri zuwa bayyanarta, duk mabiyansa suna qarqashin tsarin ne, komai wuya kuma duk runtsi ba sa saba wa umurninsa.
6) Shirye-shiryen fadada hukumar zuwa wani gari da ake kira Yathrib (Wato madina a yau) da tsara yadda za su hada daula ta bai-daya.
7) Tashin hukumar muslunci daga Makka zuwa hedikwatarta ta kanta wato Yathrib, wurin da musluncin ya canja masa suna zuwa Madina, kafin Annabi SAW ya shigo Madina komai na shugabanci a muslunce ya riga ya gama tabbata, hukuma ta gama haduwa jiran shugaba kawai take yi.
.
Duk wadannan tsare-tsare da ake yi Annabi SAW yake ba da umurni, ba a san wani daban da yake koya masa ko yake ba shi umurni ba sai Allah SW, yadda wahayi ya yi ta bibiyar juna a duk mu'amalolinsu na yau da kullum da kuma sha'anin addini wato Muslunci, Yahudawan Madina ba su ankara da lamarin Annabi SAW ba har sai da ya shigo musu, duk sauran Annabawan da aka yi a baya cikinsu ne kuma sun san qarfinsu da abubuwan da za su iya yi, bullar Annabi SAW a cikin mutane irin na Makkah ba abin damuwa ne ba a wurinsu, ko Makkawan za su iya tsare musu komai, sai ga Madinar ta zama qasar muslunci a bugun farko, qarqashin manzon qarshe da ba shi a cikin banu Isra"ilan.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248