JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 23

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 23


YAQIN UHUDU
Kafurawan Makkah sun yi shiri a wannan karon sama da na farko, domin yaqin Badar ya nuna musu cewa mutanen Madina fa ba kanwar lasa ne kamar yadda suke zato ba, tunda sun yi musu raunin da ba za su taba mantawa ba na kashe manyansu, a don haka suka yi shirin da za su muttsuke su kawai su wuce, abinda za mu karanta anan shi ne: Yaqin Uhudu ma kamar yaqin Badar ne, ba musulmai ne suka nemi a yi yaqin ba, kafurawan Makkah ne, shi ya sa ma duk yaqoqin da aka yi Makkawan ne suke zuwa Madina.
.
WA YA CI NASARA TSAKANIN KAFURAWAN MAKKA DA MUSULMAI?
Kai tsaye musulunci ne ya yi nasara, in mutum ba dan Shi'a ba ne dole ya fadi gaskiya domin a bayyane take:-
a) Kafurawan Makkah sun zo Madina ne don daukar fansar magabatansu.
b) Suna so ne su kashe manyan muslunci don rama abinda aka yi musu .
c) A qarshe su shiga cikin Madina don yaqi ya kawo su kuma sun ci nasara.
d) Za su kama bayi kamar yadda aka saba duk in an yi nasara a wurin yaqi.
e) Za su tsaya a Madina na wasu kwanaki aqalla 3-4.
.
Tabbas an rasa rayuka a yaqin sakamakon saba umurnin shugaba, wannan kuwa yakan faru a duk wuraren yaqi, sai dai kuma ga wasu tambayoyi da amsoshinsu:-
T1) Wai da gaske ne sahabbai sun gudu a lokacin yaqin Uhudu?
Amsa: Ba da gaske ba ne, duk wanda ka ji an ce ya gudu to an ci nasara a kansa, ba wasu ke yin yaqin ba sai sahabbai, in suka gudu to wa aka qarisa yaqin kenan?
.
T2) Wai sahabbai sun gudu sun bar Annabi SAW?
Amsa: Shi ma ba haka ba ne domin kuwa matsala aka samu, wadanda ke kan dutse sun tabbatar da cewa an ci nasara sai suka sauko, kafurawan suka biyo ta bayansu, na gaban kuma suka juyo, da haka aka sanya a tsakiya da sara ta gaba da baya, ba su ma ankara sun gano inda Annabi SAW yake ba bare su gudu su bar shi, ko su zo su kare shi, shedaniyar sanarwar da aka yi ta mutuwar Annabi SAW ta dada karya lagwansu, da suka gano cewa yana da rai, kuma aka yi maza wurin ba shi kariya aka daga tutar da ta fadi sai qarfin musulmai ya sake taruwa wuri gudu, amma sahabbai ba su gudu ba karatun 'yan shi'a ne?
.
T3) Don me sahabban suka bar Annabi SAW suka ranta a na kare?
Amsa: Ba fa barinsa suka yi ba, tutar da ake dagata don sanin inda 'yan uwa suke ne aka kayar da ita, duk in ana yaqi mai daga tuta ake hari don a wargaza kan mayaqa, sahabbai da dama sun mutu a kan daga tutar, ba wanda ya san inda Annabi SAW yake bare 'yan uwansa, ko su kafuran da sun san cewa Annabi SAW nanan a wannan lungun da sun zo da dawakinsu, duk dabhaka ba su amshe linzamin yaqin ba, sun dai maida hankali wurin kashe sahabbai a dalilin faduwar tuta, Annabi SAW na tsakiyansu ta gefen dutsen wajen lungun Uhudu tare da 'yan tsirarun dake tsaye tun farko tare dashi, ba wanda ya san inda yake daga musulman har arnan, Allah ya ba shi kariya, ta ina za a ce sahabbai sun gudu sun bar shi? Ana daga tuta sama suka zagaye shi don kowa yanzu ya san inda 'yan uwansa suke.
.
T4) An ce sun arce har cikin Madina.
Amsa: To me ya sa kafurawan Makkan ba su bi su har cikin Madinan sun kashe su sun kwaso mata da yara a matsayin ganima ba? Ko ganuwar Madinan ba su iya shiga ba, daganan Uhudun suka arce sai Madina, wa ya kora su kenan? Amsar dai ita ce sahabban da ake cewa sun tsere su ne dai suka kora kafuran in haka ne kuwa da wani laifi za a kama su? Ko Annabi SAW wanda suke cewa an bar shi a mahallaka ba a ji wani bayani da ya yi wanda yake nuna cewa sahabban sun gudu sun bar shi ba, sai yabo da aka yi samu, sahabbai sun yi rawar gani yadda suka jajurce suka hana kafurai shiga cikin Madina kuma suka yi musu korar kare.
.
T5) To ba warwason ganima ya dauke hankalin sahabban suka saba umurnin Annabi SAW ba?
Amsa: Ba shi ba ne, zato suka yi an yi nasara kafurawan sun gudu, ba su san cewa zagayowa suka yi musu don su yi musu qofar raguwa ba, ai yaqin ba a Makka aka yi yadda za a kwashi ababan duniya ba, ba kuma irin yaqin Badar ne da wasu kayan kasuwanci ke tare da Quraishawa ba, asali rundunar soji ce, kuma yaqin suka fito, koda an sami ganimar ma ba duk abinda mutum ya samu zai tafi da shi ba, ba wani mai kaya, tarawa za a yi wuri guda a raba gwargwadon yadda shari'a ta zartar, maganar warwaso ko kwadayi sharrin Shi'a ne da batancin sahabban Annabi SAW.
.
T6) To an kashe sahabbai kwatankwacin yawan da aka kashe wa Quraishawa a Badar wa ya yi nasara kenan?
Amsa: Yaqinnan Quraishawa sun so rama kisar da aka yi wa manyansu ne, kuma sun tambaya in Annabi SAW da Abubakar RA suna da rai, Umar RA ya ba su amsar cewa duk suna raye, kenan kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, sun kasa shiga Madina kamar yadda suka so, ba su da wata ganima, ba su iya tsayawa a wurin ba samsam bare ma su kwana, hasalima a sukwane sukabar bar wurin tare da ajiye cewa za su dawo da nufin sai sun cimma burinsu to wace nasara suka ci?
.
Annabi SAW da sahabbansa sun yi nasara don sun hana shiga Madina kamar yadda kafurawan suka tsara, sun hana tsayawa a Uhudu, ba wata ganimar da aka samu, manyan musluncin kuma sunanan da ransu, kenan sun kare martabarsu da mutuncinsu, har yanzu Larabawan yankin na da masaniyar ba a ci Madina da yaqi ba, sai wadanda suke kiran kansu musulmai ne suke tabbatar da cewa sahabbai sun gudu an ci nasara kan musulmai Allah ya kyauta, yaqin Uhudu wani ma'auni ne da yanzu haka musulmin gaskiya zai iya rabewa tsakanin zare da abawa, ba mu qi cewa an saba umurnin shugaba ba amma kowa ya san cewa su ba ma'asumai ne ba, kuma nan take an dandani sakamakon hakan, a qarshe muslunci ya yi nasara, Allah ya qara wa sahabban Annabi SAW daraja koda mushrikai da munafukai sun qi.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)