INA YAWAN WASWASI MENENE MAFITA?
TAMBAYA❓
Don Allah Malan kar na zamo Wanda Allah zaiyi fushi dasu wallahi Abunan karuwa yake, na kasa gane mene matsala ta wallahi dan Allah Dan Annabi a taimaka mun please
Kuma malam Ance ba shedan da Azumi komah ina wasiwasi koma malam Allah ne kaɗai yasan yanda nakeji wallahi bansan me yake damuna bah
Kamar zuciya tah ce take ce mun haka but malan na kasa daina wa dan Allah malan a taimaka mun wallahi haka karnaje Allah ya hukunta ni wallahi malam sainayi kukarin dai nawa but I can't.....
AMSA👇
Toh Dan uwa ina rokon Allah da ya yaye maka wannan masifa.
Toh dai daure shedanu da azumi bashi yake nuna cewa babu su ba. Bari nayi maka misali na kusa kusa, shin da azumi ba'a samun mutanen da suke shaye shaye? Shin ba'a samun mutanen da suke batsa ko wasu fitintinu na daban?! Tabas duk ana samu, kuma wannan duk sharrin shedan ne. Sboda haka daure su bashi yake nuna cewa ba sauran fitina atare da mutane ba. Wallahu A'alamu.
Toh shi dai waswasi iri iri ne, dah ya kamata ace ka bambamce wane iri kake yi.
Domin kuwa akwai waswasin da akewa addu'a akwai wanda kuma ba'a masa addu'a, wanda dakewar zuciya kawai ake buqata.
Akwai hadisin da Manzon Allah (s.a.w) yace: "idan dayan ku ya tayar da sallah, toh shedan zaizo yana masa waswasi acikin sallar, ko ya nuna masa cewa alwalarsa ta karye don ya bata maka sallah. Har wani lokacin ma ka kanji iska a tsakanin duburarka kamar kayi butu. Toh Annabi (s.a.w) yace idan kaji haka kada ka katse sallar ka har sai kaji doyin tusar ko kaji sautin fitar tusar.
Sanna sahabbai sun taba samun Manzon Allah (s.a.w) suka ce dashi "mutum ne yana sallah zai dinga ji ana raya masa cewa 'yayi butu (tusa)' yaji ana ce ma sa alwalarka ta karye a zuciyarsa. Manzon Allah (s.a.w) yace idan dayan ku yaji haka toh yace KARYA NE!
Sannan Manzon Allah (s.a.w) yace "shedan ba zai kyale dayanku ba sai ya dinga zuwa yana yi masa tambayoyi a cikin zuciyarsa. "tambayoyin da zasu jefa ka cikin bala'i" yazo ya ce maka wa ya halicci sama, sai ka ce ALLAH, yace wa ya halicci kasa kace ALLAH, wa ya halicci kaza? Kace ALLAH, toh a karshe pha zai ce ma toh shi kuma ALLAHN wa ya halicce shi??
Toh sai manzon Allah (s.a.w) yace idan kaji wannan sai ka ce:
*آمنت بالله ورسله*
"amantu billahi waruslihi"
Ma'ana
"Na yi imani da Allah da Manzanninsa"
ko kace
*هو الاول والاخر والظاهر والباطن وهو بكل شيء عليم*
"huwal awwalu wal akiru wal dahiru wal badin wahuwa bi kulli shai'in alim."
Ma'ana:
Shi ne Na farko, Shi ne Na karshe, Shi ne Bayyananne, Shi ne Boyayye, kuma Shi Masani ne da komai.
Toh kaga shi wannan waswasin ana yi masa addu'a shi kuma wancan ba'a yi masa. Saboda haka ya kamata ka tantance wane iri kake yi, duk da cewa a Alkur'ani Allah ya bamu ka'ida kwaya daya dangane da sha'anin waswasi wanda shine "isti'aza" wanda duk lokacin da kaji shedan yana taba maka zuciya toh sai kayi "isti'aza"
*أعوذ با لله من الشيطان الرجيم.*
Wanda idan ka fitinu da waswasi cikin salla ko karatu sai ka tofa a gefan hagunka sau uku...
Addu'oin korar shaidan da waswasin sa kuma Sai ka duba
Abu dawud 1/206, da Tirmizi.
Haka Imam muslim 1/291 da Bukhari 1/151.
Muslim ma ya fitar da wani idan ya ambaci "Yin zikiri (ambaton Allah) da karatun alkur'ani." 1/539.
ALLAH NE MAFI SANI
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.