KUSKURENA YA YIN DA NAKE SALLAH 09

KUSKURENA YA YIN DA NAKE
                SALLAH


🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*FUTOWA TA 👇*
            *(09)*

*DAGA MURYA A CIKIN MASALLACI*

   Yana daga cikin al'amura masu ban takaici ka samu a mutane suna daga muryarsu acikin masallaci suna wasa da hargowa, abun da yake wajibi ga mutum shine ya daga muryarsa gwargwadon bukata, ba tare da wani ya dagawa wani murya ba, saboda kowa yana ganawa ne da mahaliccinsa, kamar yadda ya tabbata cikin abun da Abi sa'idul kudri ya rawaito cewa manzan Allah saw yana i'itikafi acikin masallaci sai ya ji su suna daga murya wajan karatun Alqur'ani, sai ya daga labulan da yake ciki sai yace :KU SAURARA DUKKANINKU KUNA GANAWA NE DA UBANGIJINKU, KADA SASHINKU YA CUTAR DA SASHE KADA SASHENKU YA DAGAWA SASHE MURYA WAJAN KARATU (KO KUMA YACE) WAJAN SALLAH".
 

*ALLAH SHINE MASANI*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*MU HADU A FUTOWA TA (10)*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)