Bayan Kammala Jima'i (Sex)
_Wasu Abubuwa 10 Da Suka Kamata Ma'aurata Suyi Bayan Jima'i:_
Ba wai kawai saduwar jima'i bane yake baiwa ma'aurata ƙarin soyayya da kusantar juna ba. Akwai wasu halaye da Ɗabi'un da ma'aurata idan suna yiwa junansu duk bayan ko wane kwanciyar aure tofa a kullum zasu ƙara danƙon soyayyar auratayya su.
_Gyaran Mata Domin Maza_
+2347038308569
A wannan darasin zamu kawo muku wasu abubuwa 10 Da suka kamaci ma'aurata su kasance suna yi a duk bayan kammala jima'i.
1: Yiwa Juna Godiya: yana da kyau ma'aurata su riƙa yiwa junansu godiya a duk bayan jima'i saboda yadda kowane cikinsu ya bada tasa gudunmawar jiyar da juna daɗi.
Kuma miji da mata sun kashe sha'awarsu ne ta halak albarkacin guda.
Wannan yasa yiwa juna godiya duk bayan jima'i yana da kyau.
2: Tsaftace Al'auran Juna: Yana da kyau duk bayan kammala jima'i ma'aurata su tsaftacewa junansu jiki a ƙalla ko bazasuyi wanka ba,to suyi tsarki da ruwan ɗumi su ɗaura alwala.
3: Yin Wanka Tare: Bayan kammala jima'i yana da kyau ma'aurata su shiga suyi wanka tare.
Haka yana ƙara danƙon soyayya matuƙa ga ma'aurata.
4: Ciyar Da Juna: Akwai wanda suke son cin abinci bayan kammala jima'i.
A irin wannan ya dace koda guda baida sha'awar ci, to ya zauna tare da gudan yana ciyar dashi ko suna ciyar da juna.
Wannan salo na soyayya bayan jima'i yana ƙara kusantar ma'aurata.
5:Tattaunawa Akan Jima'i : A wannan lokacin yana da kyau ma'aurata su taɓa batun jima'i n da suka kammala a yanzu. Idan akwai abunda aka yi wa guda da bai gamsar dashi ba sai yayi magana.
Idan kuma dukkaninsu sun samu gamsuwar da suke buƙata sai sun kambama juna tare da jandadawa juna salon kwanciyar da suka fi buƙata ko kuma Wasannin Motsa Sha'awa.
Irin wannan hiran yakan baiwa ma'aurata daman gano abunda suke so da kuma abunda suke ƙi a lokacin jima'i.
6: Kwanciya Tare: bayan kammala jima'i yana ƙara shaƙuwar ma'aurata.
Ya dace duk bayan jima'i kada kowa ya koma ya kama shifiÉ—arsa daban sai kuma lokacin jima'i ne zasu sake haÉ—ewa kuma.?
7: Rungumar Juna: Bawai kawai ma'aurata su kwanta a shimfiÉ—a guda ya wadatar ba.
Yana da kyau miji da mata su rungumi juna a yayin kwanciyar tasu.
8: Yiwa Juna Kalaman Soyayya : Idan an rungumi juna ba kuma gum za ayi ba kamar kurame ba.
Yana da kyau a wannan lokacin ma'aurata suna shafa juna suna kuma zuga juna na kyau ni'ima ko halitta da kuma soyayyar da suke nunawa juna.
9: Addu'ar Kwanciya Barci: Ma'aurata su Tunasar da juna Addu'a kafin barci ya É—auke su.
10: Sumbatar Juna: Kada ma'aurata su sake barci ya kwashe su ba tare da sun yiwa juna Sumbatar ƙarshe ba.
Da zaran ma'aurata sun ji alamun barci na zuwa. Wannan good night kiss ba ƙaramin tasiri bane yake dashi a tsakanin ma'aurata ba.
Da fatan ma'aurata zasu daure suyi amfani da waÉ—annan matakan