ƊAN'DAM DA RIƘIƊA IRIN TA HAWAINIYA !!

ƊAN'DAM DA RIƘIƊA IRIN TA HAWAINIYA !!


• Za su kauda kai daga gareka, a lokacin da ba sa ganin komai a goshinka sai duhu (lokacin da kai ba komai ba ne), sa'an nan kuma ai ba ka da komai na abin ba su. Abin dake zuciyarsu a lokacin, shi ne; kaima ka ji da kanka!👌

• Amma idan lokaci ya yi, Allah ya nufi goshinka ya yi haske; to, sune fa za su fara bayyana irin hasken dake goshinka (a lokacin da ka zama komai), daga wannan lokacin za su kusance ka; ba don a baya ba su sanka ba, sai domin ba ka gabansu. Ma'ana ba ka da komai, ba su tsammaci kuma za ka zama komai ɗin a yanzu ba.

• Irin waɗannan idan da hali; kar ka haska su da hasken goshinka, domin ba sa nufinka da alheri. Sun zaɓi su kusanceka ne saboda sauyin da Allah ya bayyana a tare da kai, da sun tsammanci hakan, da sun so ka tun da farko.

• A yanzu idan sun soka, domin hasken goshinka da suke gani; kai da wane irin matsayi kake kallon su?

Note:👇
Idan da hali, ka ƙaurace musu, idan ba hali, ka yi hankali da su. Ka kiyaye su.

Suna da lafazi mai kaifi...
Ba sa yanka ko'ina, sai idan sun shirya, sa'an nan ne za su yanka, wanda sai sun tabbatar idan har sun ɗora, to, za su ga jini.

NASIHA CE !!!

©Uthman Ibrahim Khalil
Post a Comment (0)