HAƘIƘANIN KOMAWA GA ALLAH (SWT)

Haƙiƙanin Komawa Ga Allah (SWT)

08/December/2020


A wannan mawiyacin halin da al'umma take ciki, ana yawan nanata cewa mafita ita ce a koma ga Allah, Sai dai wasu suna yiwa wannan maganar wata gurgurwar fahimta suna taƙaita komawar ga Allah a iya Sallah da Azumi da sadaka da nafilfilu da sauran ibadu da suke takaita ga mutun, wanda wannan baragurbin tunanin ya sa wasu masu jin haushin addininma sun fake da shi wajen sukar shi kansa Addinin da masanansa, suke kokarin nuna cewa addinin ya gaza. Hakanan wannan tunanin ya yi daidai da matsayar ƴan ba ruwan Allah ( Secularists) na takaita addini a masallaci ko iya alakar mutun da Ubangijinsa, da kuma zare addinin daga rayuwarsa ta yau da gobe.

Lallai komawa ga Allah bai takaitu kawai a yin salloli da nafifilu da addu'o'i ba kawai duk da mahimmancinsu, sai dai komawa ga Allah bayan aikata waɗancan abubuwan ya haɗa da aikata umarninsa na tashi tsaye domin neman mafita da ƙoƙarin magance waɗannan matsalolin domin dole sai mutanen ne za su tashi su yi aiki tukuru su gyara ba wata mu'ujiza bace za ta bayyana ko mala'iku bane za su sauko daga sama su gyara musu ba.

Yana daga cikin komawa ga Allah ko wane shugaba ya yi iya ƙoƙorin sauke haƙƙin da Allah ya ɗoramamai na al'ummarsa, ya yi duk abinda zai yi wajen kareta da amfanar da ita da kawo mata cigaba. Tasirin shugaba yana da ƙarfi sosai ƙwarai da gaske a cikin al'umma duk san da ya zama na gari to wannan nagartarar tasa tana tasiri akan al'ummarsa san da kuma ya zama na banza to wannma yana tasiri akan al'ummarsa, Alkur'ani da Tarihi shaida ne cewa mutane Suna kan adddinin Shuwagabanninsu ne, ba Shuwagabanni bane suke kan addinin talakawansu ba, domin duk da yadda al'umma takai ga nagarta to matukar shuwagabaninta na banzane to ba abinda zata iyayi, sannan tarihi yana nuna mana cewa akan iya samun shugaba na banza al'umma tagari wanda wannan shine halin kasashen musulmai a yau don galibin talakawan da ake mulka sun fi shuwagabannin da suke mulki nagarta. Na taɓa bayanin wannan batu dalla-dalla tare da bada misalai a wani rubutu da ya taba gabata.

Hakanan yana daga cikin komawa ga Allah ga talakawan da ake mulka kowa ya yi koƙarin sauke haƙƙin da Allah ya ɗora masa na tarbiyantar da waɗanda suke ƙarƙashinsa hakanan da yaɗa umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, domin hakan zai rage yaduwar barna da fasadi, hakanan yana daga cikin komawarsu ga Allah su yi ƙoƙarin zaban shuwagannani nagari waɗanda suka cancanta waɗanda al'umma za ta amfana in ma ba ta amfana ba to aƙalla ba za ta cutu ba, in kuwa suka yi akasin hakan to duk wani bala'i da za su fada to su ne suka janyowa kansu, kuma har da su Allah zai hada ya yiwa hisabi, domin sun bada gudunmawa.

Lallai aiwatar da hakan shine cikakken komawa ga Allah, yin ayyuka nagari da ƙauracewa munana tare da tash da aiki tuƙuru wajen neman mafita da kawo gyara, da wannane za a samu gyara, wannan ita ce sunnar Allah ga mumunai. Ita kuma sunnar Allah bata taba canzawa.

#Abm_Sani

https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml
Post a Comment (0)