HAKURI A GIDAN MIJI ZAI GADAR MIKI KARSHE MAI KYAU DA KUMA NASARA DUNIYA DA LAHIRA.
Shaikh Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa; "Idan har mata tayi hakuri tanemi lada awurin ubangijinta sannan tayi dakon mafita daga wurin Allah, takuma sauke hakkin mijinta da Allah ya dora mata koda kuwa shi mijin ta tauye mata nata hakkin, to lalle nasara da kyakykyawan karshe na gareta. Wanda kuma wannan itace qa'ida ga duk wanda yakeda hakki akanka, idan har kai ka sauke naka hakkin shikuma yaki saukewa to sai Allah ya doraka akansa.
Dalili kuwa hadisin manzon Allah, wanda sahabi Abu huraira ya ruwaito yace "wani mutumi yazo wurin manzon Allah yace: ya manzon Allah na kasance inada yan uwa wadanda ina sadar musu da zumunci amma su suna yankemin, ina kyautata musu, amma su suna munantamin, ina hakuri dasu amm su sunamin jafa'i. Sai manzon Allah ya ce masa "*Idan har ka kasance kamar yadda ka fada to kananan kamar kana ciyar dasu tokace Mai zafi, kuma bazaka gusheba Allah yana baka kariya da taimako ba har abada matukar kananan ahaka baka sauya ba"
مسلم ٢٥٥٨
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/