HUKUNCIN AMSA SALLAMAR WANDA BA MUSULMI BA
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min.
Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki?
kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama idan yace ma Assalamu alaikum?.
Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata.
daga dalibinka Ibraheem I g
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Allah Maɗaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu.
Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI".
(Ma'idah ayah ta 51).
Ibnu Abi Hatam ya ruwaito cewa Watarana azamanin Khalifancin Sayyiduna Umar (rta) ya ce ma Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (rta) ya rubuto masa wani abu.
Shi kuma Abu Musal Ash'ariy sai ya sanya wani kirista (Nasaara) ya rubuta masa. Daga karshe da Sayyiduna Umar ya gane hakan sai da yayi masa fa'da sosai. Sannan ya tunasar dashi wannan ayar da muka kawo a sama.
Babu laifi ka kyautata alakar zamantakewa tare dasu awajen aiki ko kasuwa. Amma kar ka rikesu amatsayin abokai ko aminai gareka.
2. Dangane da amsa sallamarsu, akwai maganganun Malamai kala-kala. Amma magana mafi rinjaye ita ce wacce Ibnul Qayyim ya kawo acikin ZADUL MA'AD juzu'i na 2 shafi na 425-426, yace :
"Malamai sunyi sa'bani dangane da wajibcin amsa sallamar wanda ba Musulmi ba (idan yace maka Assalamau alaikum) amma Mafiya rinjayen Maluma sunce wajibi ne. Kuma wannan shine ra'ayi mafi Sahihanci.
Sannan Malaman sunce zaka mayar masa da cikakkiyar Sallama ne bisa gwargwadon yadda Allah yayi umurnin cewa :
"IDAN AKA GAISHEKU DA WATA GAISUWA, TO KU MAYAR DA IRIN WACCE TAFI KYAWU, KO KUMA KU MAYAR DA ITA (KAMAR YADDA AKA YI MUKU)".
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ