DUNIYAR MUTUWA // 04
.
Dukkanin mu sai hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa’iku da mu ka ga sun zo sun wuce mu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskin da ban taba shaaqar tamkarsa ba a rayuwata. Na cewa Malaa’iku: Wanene wannan? Ni dai ban da na san cewa Annabi Muhammad S.A.W shi ne qarshen Annabaawa, da na ce wannan Ruhin Annabi ne! Saboda Rakiyar Malaa’iku da na gani sun mata, da Qamshinta gami da yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!
.
Sai suka ce: wannan Ruhin shahidi ne da yayi shahaada a Palastine, dazunnan Yahudawa suka kashe shi, yana mai kaariya ga Addininsa da Garinsa, haqiqa Allah ya sa yanada yawan Ibaadah ga shi Mujaahidi! Sai na ce: Kaicona ina ma ace nayi mutuwar Shahaadah ne!
Ba’a jima ba sai na ga wasu Malaa’ikun dauke da wata ruhi abar qyama, wani wari mai doyi na tashi daga gare ta! Sai na ce waye wannan?
Sai suka ce: Wannan Mutumin Handusa ne, yana daga cikin masu bautar shaanu, ya mutu ba da jimawa ba bisa tsawa da Allah ya turo musu, sai na gode Allah bisa ni’imar Musulunci.
.
Sai na ce musu: Wallahi duk yanda na karanta wadannan abubuwa, ban yi zatonsu haka ba, sai Malaa’ikun suka ce: Bushaararka da Alkhairi, amma ka sani Al’amarin da ke gabanka mai tsayi ne. Sai na ce ina mai mamaki: Yaya kenan? Suka ce: Duk zaka ga haka, sai dai munaso ka kyautata zatonka ga Ubangijinka. Muka wuce wata jamaa’ah ta Mala’iku mu kai musu sallama, sai suka ce: waye wannan? Sai Mala’ikun suka ce: wani mutum ne musulmi, dazun nan yayi hatsari sai Allah ya Umarce mu da mu je mu dauko ransa daga Mala’ikan mutuwa, sai Malaa’ikun suka ce: Lallai Allah mafi ni’ima ne da Karamci ga Musulmai, domin su Alheri ne kuma Alheri ne qarshensu!
.
Sai na cewa Mala’ikun nan 2: suwaye wadannan? Suka ce: Wadannan Mala’ikun su ne masu gadin sama, kuma su ne masu wurga shahab (taurari da ake jifan aljanu da su) ga shaidanu! Sai na ce: Lallai halittarsu mai girma ce. Sai suka ce: ai akwai wadanda suka fi su girma ma! Sai na ce: su waye? Suka ce: Jibril da masu riqo da Al-arshi! Kuma su halitta ne daga halittun Allah ba su saba masa bisa umarninsa kuma suna aikata abin da aka umarce su!
.
Na ce: Tsarki ya tabbata gare ka ya Allah, haqiqa ba mu bauta maka ba kamar yanda ya kamata! Sannan muka isa saman Duniya, haqiqa na kasance tsakanin shauqi da mamaki! Saboda abin da na gani, kuma tsakanin tsoro da da firgici. Na ga saman duniya mai girma ce matuqa, tana da qofofi a rufe, akan kowace qofa akwai Mala’ika mai matuqar girma a tsaye, sai Malaa’ikun nan 2 suka ce: Assalamu alaikum, ni ma nai sallamar tare da su, sai suka amsa mana: Wa’alaikumus-salaam, suka ce: maraba da Malaa’ikun rahmah, suka dube su suka ce: ba makawa wannan Musulmi ne! Suka ce: Tabbas kuwa, sai Malaa’ikun (dake gadin qofofin sama) suka ce: ku shigo, domin ba’a bude qofofin sama face ga Musulmai, domin Allah na cewa: ((Lallai ne wadanda suka qaryata ga ayoyin mu, kuma suka bijire mata, ba’a bude musu qofofin sama, kuma baza su shiga Aljannah ba har sai raqumi ya fita ta kafar Allura, hakan ne muka sakankawa masu laifi)) A’araaf:40.
.
Sai muka shiga, na ga abin mamaki, na ga wani gini babba tamkar Ka’abah, Mala’iku masu yawa na dawafi akewayenta, na ce: wannan lallai shi ne “BAYTUL-MA’AMUR” Mala’ikun su kai murmushi suka ce eh, Alhamdulillah, mafi yawan wadanda muka zo da su nan daga Musulmai suna gane wannan wuri, wannan kuma falalar Allah ne kuma falalar Mutumin qwarai Annabinku Muhammad S.A.W wanda bai bar wani abu ba face ya ya sanar da ku! Sai na ce da su: Mala’iku nawa ne ke zuwa nan kullum? Suka ce: Dubu 70, kuma da sun wuce ba sa dawowa! Sai muka daga cikin tsananin sauri zuwa sama ta biyu.
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248