KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 16


KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 16
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa 
.
ƘA'IDOJIN ISAR DA SAƘONNI A MUSULUNCI
8. Mu yi amfani da waɗannan kafofi wajen inganta fahimtar addini da kyautata imaninmu, kuma mu yi alaƙa da malaman ƙwarai da ɗaliban ilmi, waɗanda saƙonnin da suke yaɗawa yake cike da tsantsan ilmi da tsoron Allah.
.
Mu yi amfani da kafofin zamani don ƙarfafa zumunta tsakanin ƴan'uwa dangin zumunta. Haka kuma tsakanin abokai, maƙwabta da sauran jama'a, kuma mu kasance masu alaƙa da waɗanda suke da manufa ta yaɗa ayyukan alkhairi da kyautatawa a tsakanin mutane tare da kuma yaƙi da ayyukan ɓarna da fasadi a cikin al'umma.
.
Allah (S.W.T) Yana cewa:
إن الله يأمر بالعدل والإحسان وإيتاء ذي القربى وينهى عن  
                           .الفحشاء والبغي يعظكم لعلكم تذكرون                 
"Lallai Allah na yin umurni da adalci da kyakkyawa, da bai wa ma'abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka ƙi da rarraba jama'a, Yana yi muku gargaɗi, tsammaninku kuna tunawa".
Suratun Nahl: 90.
.
9. Mu kula da wajen kaucewa isar da dukkan saƙon da ya kai gare mu ba tare da cikakken bincike ko fahimtar al'amura ba. Mu tuna da faɗin Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya isa aikin zunubi mutum ya ce zai mayar da dukkan abin da ya ji". Don haka idan mutum zai yi amfani da kafar sadarwa don tura wani saƙo, ya tsaya ya tambayi kansa, shin abin da nake ƙoƙarin turawa zai amfani waɗanda zan tura wa zuwa gare su ko a'a?
.
10. Mu kiyaye da ƙa'idar binciken dukkan saƙon da ya zo gare mu cewa; shin na gaskiya ne ko saɓanin haka? Sau da yawa mutane na gaggawar tura saƙo ga abokan hulɗarsu ta kafofin sadarwa da zarar wani ya turo musu wannan saƙon ba tare da tantance sahihancinsa, alhali kuma Allah Ya gargaɗi bayinsa Muminai da su kasance masu tantance sahihancin bayanai kafin isar da su.
.
Allah (S.W.T) Yana cewa:
ياأيها الذين آمنوا إن جاءكم فاسق بنبإ فتبين أن تصيبوا 
                    قوما بجهالة فتصبحوا على مافلتم نادمين
"Ya ku waɗanda suka yi imani! idan fasiƙi ya zo muku da labari, to ku nemi bayani domin kada ku cuci waɗansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuna masu nadama".
Suratul Hujurat: 6.
.
.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)