LABARI»»» 02

LABARI»»» 02


DA JUNA BIYU TA TARE A GIDANSA

Yayin da aka idar da sallar Asuba, sai liman ya tare shi, ya yi masa magiya ya hada shi da Allah cewa: “Wane aiki yake yi na alheri, domin ya yi mafarki ba sau daya ba yana ganinsa a cikin aljannah”. Kuma liman ya rike wuta duk da dagewar da mutumin yake kokarin yi na kin gaya masa. 

Can sai mutumin ya nisa ya ce: “Zan gaya maka amma da sharadi, cewa ba za ka gaya wa wani”. Liman ya yarda da sharadi. 
“Ranar da aka kawo mini matata na tarar tana da ciki wata biyu ko uku” in ji wannan mutumin. “Yayin da na fahimci haka sai na ki kusantarta, tausayinta ya kama ni na tunanin idan asirinta ya tonu. Gari na wayewa sai na shirya muka bar garin zuwa wata jaha da ba a san mu ba, haka muka zauna tare da ita. Da yake ba wanda ya sanmu a garin, babu wanda yake shigowa gidanmu, ni kuma da safe sai in tafi kasuwa in dan sayi abubuwa in sayar, tun da dama ni dan kasuwa ne”. 

“Haka muka zauna muna renon wannan ciki har Allah Ya kawo ranar da za ta sauka. Da rokon Allah haihuwa ta zo cikin dare, kuma ba tare da wata wahala ba”. Mutumin ya ci gaba da cewa: “Karfe uku da rabi na dare, sai na dauko wannan jariri, na ajiye shi a kofar masallaci na koma gida”. 
 “Bayan ladan ya fito mutane sun fito sallah sai suka ga jariri, aka taru ana ta kace-nace a kansa, sai na fito na tarar da taron masallata, sai ni ma na shiga cikin masu ta’ajibi, can sai na ce: Don Allah a ba ni shi in rike, saboda ba ni da da. Nan take kowa ya amince, kuma kowa ya yi murna ya yi mana addu’a. Na dauko yaro na dawo da shi gida”. 

Bayan nan sai muka tafi wani gari, limamin garin ya sake daura mana aure. Sai na komo da ita gida, da mutane suka tambaye ni game da yaron sai na ce dan wani abokina ne da muke tare, saboda rashin matarsam aka nemi matata ta rike shi. Haka muka zauna tare da ita ba tare da wani ya sani ba, Allah Ya bata wasu ‘ya’yan, yaro ya taso tare da su, amma Allah bai sa mai dogon kwana ba ne sai ya bar duniya”. 
Ban da kai yanzu da ka hada ni da Allah, ban taba gaya wa wani wannan lamari ba, saboda haka ka rufa mini asiri, kuma wannan shi ne labari na. 
.
.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda rufawa wani Musulmi asiri a duniya Allah zai rufa masa asiri a duniya da lahira, kuma duk wanda ya yayewa wani musulmi wani kunci a duniya, Allah zai yaye masa kuncin duniya da na lahira”. Musim


Daga 
MIFTAHUL ILMI

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)