KUSKURENA YA YIN DA NAKE SALLAH 14

*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *SALLAH*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*FUTUWA TA 👇*
           *(14)*



  *RUBUTA AYATUL KURSIYYU DA FALAQI DA NASI DA MAKAMANTANSU AJIKIN MASALLACI*

   Yana daga cikin kusakurai da ake yi shine rubuta sura ko ayar qur'ani ajikin bangon masallaci, an tambayi Imamu Malik shin me kake gani dan gane da rubuta ayatul kursiyyu ko falaqi da nasi ko makamancin su acikin masallaci? Sai yace ina kyamatar rubuta wani abu daga cikin Alqur'ani jikin alqibla ko wani ban gare na masallaci, domin hakan yana shagaltar da mai sallah. 
   Abu Ammar albarudi yana cewa aikata hakan da makamancin sa yana daga cikin kawata masallaci wanda kuma farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullah saw ya hana.

*ALLAH SHINE MASANI*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*MU HADU A FUTOWA TA (15)*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)