KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 21


*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *ALWALA*

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA👇*
         *(21)*


*WASU WASI WAJAN WARWARE ALWALA*

    shaidan yana zuwarwa dayanku sai ya dunga jin wani abu kamar acikin cikinsa yana kadawa sai ya dunga masa kokonto kamar ya futar da wani abu ko bai futar ba? sai yaje ya sake Alwala saboda tunaninsa cewa Alwalarsa ta warware amma sunnar farin jakada (saw) tazo da sabanin haka kamar yadda muslim ya rawaito daga Abu huraira yake cewa "Idan dayanku yaji wani abu acikin cikinsa sai yai tai masa kokonto shin ya futar da wani abu ko bai futar ba kada ya futa daga cikin masallaci har sai yaji sauti ko yaji wari ". 
   A hadisin abi sa'idul kudri kuwa cewa ya yi manzan Allah (saw) yana cewa shaidan yana zuwarwa dayanku lokacin da yake sallah sai ya yi masa busa acikin duburarsa sai ya dunga jin kamar ya futar da wani abu to kada ka futa har sai kaji sauti ko kaji wari ". A cikin ruwayar abu dawud kuwa cewa ya yi "idan shaidan yazo wa dayanku lokacin da yake cikin sallah sai yace dashi kayi hadasi sai manzan Allah saw yace kace dashi qarya kake sai dai idan yaji wari da hancinsa ko kuma yaji qara da kunnuwansa ". 
   Shi yasa babban malami ibn hazam yake cewa anso da mutum bayan ya gama fitsari ya yayyafa ruwa akan wandansa domin ya ijewa kansa waswasin shaidan, ya yin da ji danshi sai yace ai wannan danshin ruwan da na yayyafa ne dazu bayan nagama Alwala. Kamar yadda Abu dawud ya rawaito cewa manzan Allah saw ya kasance idan ya yi Alwala yana yayyafa ruwa ajikin wandansa.

   

*ALLAH SHINE MASANI*


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 22*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏


Post a Comment (0)