KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 20


*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *ALWALA*

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA👇*
         *(20)*


*ALMUBANZARANCI DA RUWA YA YIN ALWALA*

    Yana daga cikin shiriyarwar manzan Allah (saw) taqaituwa wajan amfani da ruwan Alwala da wanka, akwai wadanda shaidan ya jarrabesu wajan amfani da ruwa mai yawa wajan Alwala, shi yasa ibn jauzi yake cewa daga cikin wadanda shaidan yake jarrabarsu da amfani da ruwa mai yawa suna afkawa cikin abubuwa guda hudu na farko bata lokaci cikin abun da bashi da fa'ida, sabawa shari'ah wajan amfani da ruwa mai yawa akan yi da kadan, shiga cikin hani wajan qara wanke gabobi sama da sau uku, na qarshe Almubanzaranci, sau da yawa mutum yana dadewa wajan yin alwala har ya rasa raka'ar farko ko karatun fatiha ko kuma kabbarar harama ko kuma jam'i gaba daya, manzan Allah (saw) yake cewa yana isa Alwala muddu daya, wanka kuwa kwano daya.


*ALLAH SHINE MASANI*


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 21*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)