WASU MATAN // 08

WASU MATAN // 08
.


Dalibata ce kuma ba tason ta rasa darasina ko kadan, duk da cewa ba ita ta gaya min ba amma na fahimci hakan a maganganunta, sai na saka laccata ranar Asabar, ta ce "Malam ina da matsala"
.
A ganina ba yadda za a yi mu daga laccar don matsalarta ita kadai, sai dai na saurare ta, ta ce "Wallahi malam, maigidana ba ya qasar, shi ya sa duk ranar Asabar da Lahadi nake kwasan yara mu je wurin mahaifiyarsa mu wuni mata, mu dafa abincin ranakun dukun, mu yi mata wanki da guga wanda zai kai ta wani mako, mu gyara mata gida!" Gaskiya na daga laccar a kan wannan dalilin, duk da cewa na yi watsi da wasu dalilai da dama da wasu suka kawo.
.
Abinda ya sa haka kuwa na ga wata mata da ta maida uwar mijinta kishiyarta wai don danta yana yawan kula da ita, abinci ma da ya so a riqa dafawa ana kai mata ya gagara, 11 na safe kan yi ba ta karya ba, na rana kuma sai bayan la'asar, na dare ne da yake yakan bi gidan kafin ya dawo ake kaiwa a kan lokaci, shi ne ake saka nama, kuma a sanya a kwano mai kyau, a zuba da dan dama, na daren take ragewa ta dumama da safe.
.
Uwar mijinnan ta haifo wanda kike cin arziqinsa ke da 'yan uwanki da uwayenki, komai sai wanda ya rage uwarsa take samu ya kamata ki ji tsoron Allah, ba ki ganin in ya farka za ku shiga halin ni-'ya-su? 'Yan uwanta dai a gidan suke tun dadewa, har ya zama mijin ne bare, in ba yaran da suka tara yanzu ba, ko su yaran in suka ce grandma uwar mamansu suke nufi don ita suka sani, alhali uwar baban tana da rai.
.
Yanzu dai dole ma ya dawo da uwarsa gidansa wai aiki ya yi masa yawa ba zai iya zuwa gidanta kullum ba, shi kam yana da gaskiya a yadda na san shi, duk da haka uwarsa har yanzu ita take dafa abincinta saboda gudun wulaqanci, ta wanke kayanta da kanta.
.
Neman zama lafiya ya sa uwar ta koma 'yar aike ko ma'aikaciya don dai ta sami damar sararawa a gidan danta, matar tana bin duk hanyoyin da maigidan zai san abin dake faruwa ta toshe, kuma ta gyara halinta ta kyautata wa maihaifiyar ta qi, wasu matan sam ba ka iya gane mai laifi tsakaninsu da mahaifansu, tunda mahaifan suna gani ana cutar da uwar wanda suke cin arziqinsa ita da 'yan uwansa, dacewa ya yi su tsawata, sai suka ja bakinsu suka tsuke. 
.
Me ake yi da irin wadannan matan?


Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)