KUSKURENA YA YIN DA NAKE SALLAH 16


*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *SALLAH*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*FUTUWA TA 👇*
            *(16)*

*KAURACEWA YIN SALLAH A MASALLACI*

   Aikata hakan yana daga cikin mafi girman bid'ah da wasu daga cikin mutane suke aikata hakan a wannan zamanin, hakan ya zama ruwan dare muta ne sun kauracewa masallatai ya yin lokutan sallah, sun mai da guraren hirarsu da guraren aiyukansu a matsayin masallatai. 
   Mutanan da suke aikata haka su sani cewa suna aikata bid'ah ne kuma tabbas suna kan bata saboda Allah subhanahu wata'ala yana cewa "kadai wadanda suke raya masallatan Allah, sune wadanda sukai imani da Allah da kuma ranar alqiyama, kuma suka tsaida sallah suka bada zakkah babu wanda suke jin tsoro face Allah subhanahu wata'ala, wadannan tabbas zasu Kasan ce daga cikin shiryayyu". 
   Haka zalika ibn mas'ud yana cewa "Duk wanda yake san ya hadu da mahaliccinsa lafiya to ya ki ya ye salloli akan lokaci duk lokacin da aka kira su, domin Allah subhanahu wata'ala ya sunnantawa Annabinsa sunnoni na shari'ah kuma wadannan suna daga cikin sunnoni na shari'ah". 
   Haka zalika An rawaito daga Abu Huraira "wata rana wani makaho yazo wajan farin jakada babba dan Abdullahi (saw) akan cewa bashi da dan jagora wanda zai dunga kawo sa masallaci sai ya tambayi manzan Allah saw akan ya ran gwanta masa ya yi sallah acikin masallaci sai ya ran gwanta masa, ya yin da ya juya ya tafi sai manzan Allah saw ya kira wo sa sai yace dashi, shin kana jin kiran sallah sai yace masa eh, sai manza Allah saw yace ka amsa wato kazo masallaci "
   Makaho mara ido da bai da dan ja gora ba'a basa dama ba da ya yi sallah acikin gida ba, ya yin da yaji kiran sallah ya ka ke gani ga mutum mai ido? 
    Haka zalika sha'abi yace wata rana muna zaune acikin masallaci sai aka kira sallah, sai wani mutum ya tashi ya futa daga masallaci sai abu huraira ya bisa da kallo ya yin da ya futa, sai yace amma kunga wannan haqiqa ya sabawa baban Alqasim. 
  Haka zalika mu'az ya rawaito cewa "Jafa'i yakai jafa'i, kafurci ya kai kafurci, wanda zai ji an kira sallah amma yaqi zuwa ". 
  Haka zalika an sake rawaitowa cewa "ya ishi mumini ta bewa da rashin arziqi, ya ji ladan ya kira sallah amma ya qi zuwa ". 
    Don haka 'yan uwa wadanda suke yin sallah acikin gidansu ko kuma a guraren ayyukansu, da suji tsoran Allah subhanahu wata'ala su dai na aikata hakan. 

*ALLAH SHINE MASANI*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*MU HADU A FUTOWA TA (17)*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)