WASU MATAN // 09

WASU MATAN // 09


Ta fadi qarara cewa ba ta son wanda za a aura mata, amma uwayen ba su kula ba, Allah kadai ya san dalilin da ya sa suka kafe sai dai ta auri wani, a qarshe wanda suke so din suka aura mata, tsakani da Allah ba zan iya cewa me ya sa mijin ya dauki wani irin mugun mataki ba, haquri ne ko mugunta ko me? Allah ne kadai ya sani.
.
Ta haifi yara 4, daya ya rasu, 3 sunanan da ransu, a cikin 3 dayan ubansa Inyamuri ne, sauran biyun kowa da ubansa, a taqaice dai mijin bai da da ko qwara daya a cikinsu, duk haifa masa su aka yi, kuma ya san haka.
.
A binciken da muka yi mun gano cewa yana sane da cewa 'ya'yan ba nasa ba ne, don ko kadan bai saduwa da ita duk tsawon wannan lokacin, bai sake ta ba, bai kai qararta wurin kowa ba, wani sa'in ma a gan shi da yaran, matar ce ma take cewa bai damu da lafiyarta ko na 'ya'yanta ba, amma yana ba su abinci, shi dai zai ga ta yi ciki ta haihu, ya ba da abin da za a yi suna a yi shagali a watse, a islamiya ko boko da sunansa suke aiki.
.
An dai ga daya daga cikin yaran ya yi mugun kama da maqwabcinsu, har da hasken fatar, ga mijin da matar baqaqe, kowa ya ga yaron ya san ubansa, abinda zai dada tona musu asiri takan tsaya ta yi magana da shi, duk da cewa ba wanda zai qarar ko akwai wani abu a tsakaninsu don ba a sheda ba, mutane suna cewa dansa ne, kuma ba ya iya musawa.
.
Ita da kanta lokacin da take fadin ta gaji take zayyana irin cutar da halin ko-in-kula da mijin yake nuna musu ita da 'ya'yanta, ta ce yara 2 ubansu guda, daya ya mutu saura daya, su kuma saura biyun kowa da ubansa, ta ce wanda yake nesa binsa take yi can ya biya buqatarsa ya biya mata nata, shi ma Inyamurin haka, maqwabcin ne dai yake biyowa ta taga da daddare kafin maigidan ya dawo, da haka ta tara sauran yaran 3.
.
A ganina wasu matan suna kuskure, in ba sa son namiji bai nufin rayuwarsu ta lalace kenan yadda za su bar wa 'yan baya abin kunya, yanzu dai sai dai ta bar garin da yaran su koma wani wuri, in ba haka ba zai yi wahala ta sami miji komai tubanta kuwa, yaran kuma an riqa yi musu kallon 'ya'yan mutu'a kenan, sa'anta ma da yake maza ne.


Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)