WAWA SHIKE SAKIN MACE AKAN ABUNDA BAI KAI KOMAI BA
Dawud bin Abi Hindi Allah ya masa rahama yana cewa "Na zauna da fuƙaha'u (malaman fiƙhu) sai na tarar da addini na awurinsu, Na zauna da masu wa'azi sai na tarar da tausasar zuciyata awurinsu, Na zauna awurin mafiya sharrin mutane sai na tarar da ɗayansu yana sakin matar sa akan abunda bai taka kara ya karya ba".
جواهر العلم ٤٥٨
Ya kai ɗan uwa ka sani sakin mace ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba ba halin muminai bane, ya zo acikin hadisin Sahabi Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda, manzon Allah yana cewa; "Kada mumini ya tsani mumini ko ya ƙyamaceta, idan har ya ƙyamace wani hali daga gareta to ai ya samu wani hali awurinta da yake o".
صØÙŠØ Ù…Ø³Ù„Ù… ٢٧٦٤
Ma'ana a duk lokacin da takasance tana aikata wani abu da baya so to yayi dubi zuwa ga wasu halaye nata masu kyawu da suke burgeshi, hakan zaisa ya mata adalci kuma hankalinsa ya kwanta.
Ya Allah ka dawwamar da soyayya da fahimtar juna a tsakanin duk wasu ma'aurata. Ameen
#Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah