MACCE πŸŒΈπŸƒ

MACCE πŸŒΈπŸƒ


Addinin musulunci addini ne da yake koya mana Tarbiyya da kyawawan halaye da dabi'u na gari wanda zai tabbatar da mu cikin rayuwa mai dadi da (hutun zuciya)anan duniya da lahira.

Kamewa, kunya, suturcewa ita ce dabiar da aka San mace da ita, cakuduwa da maza da ba muharramai ba, ko maida su abokanai da wasa barkatai da maza, da sakin jiki a kan hanya da yawan dare-reku a hanya da ko wani namiji wannan ba dabi'a bace mai kyau, mace tana da mutuncin da daraja killace kai da 'boye kanta da suturcewar ta shine yake kara mata daraja da kwarjini da mutuntaka, shi yake kara bata kariya daga cutarwa, Tarbiyya da kula da cikakken 'yanci da addinin ta ya lullube ta da shi, hatta yadda zata yi tafiya a hanya sai da aka koya mata.

  #Zaurenfisabilillah 

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)