JININ AL'ADA 03

*JININ AL'ADA.........*

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*FUTOWA TA 👉03*

*MEYE HIKIMAR DA YASA MATA SUKE YIN JININ AL'ADA*

    Babu wani abu da ubangiji yake yi ba tare da hikima ba duk da cewa kai a matsayinka na dan adam ko ka fahimci hikamar ko baka fahimta ba wajibi ne kayi imani da shi. 
    Malamai sun yi bincike domin gano hikimar da yasa mata suke yin jinin Al'ada suke cewa a duk watan duniya ana samun kwayoyin haihuwa acikin mahaifar mace wanda wannan kwayoyin idan sun hadu da maniyyin da namiji sai ubangiji ya kasantar da dan Adam, idan kuwa wadannan kwayoyin basu samu haduwa da maniyyin da namiji ba sai su lalace su dunga zubar da jini, idan kuwa suka hadu da wannan maniyyin sai wannan jinin ya zama abincin yaron acikin mahaifiyarsa domin a wannan lokacin bazai yuwu shi jariri ya dunga cin abinci irin abun da wanda yake waje yake ci ba, abincin zai dunga kai wa zuwa garesa ta tsakankanin cibiyarsa zuwa jikinsa har zuwa lokacin da Allah subhanahu wata'ala zai fito dashi zuwa duniya. 
   Wannan shine abun da malamai suka fada dan gane da hikimar da yasa mata suke yin jinin Al'ada. 

*MUHADU A FUTOWA TA GABA*

*Rubutawa.... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi*
             *Nazifi Yakubu Abubakar*
               *Abu Rumaisa*
                  🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)