JININ AL'ADA: GABATARWA


*JININ AL'ADA...........*

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*GABATARWA...........*


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga mahaliccimmu wanda ya bamu dama da iko na rubuta wannan littafin mai suna *JININ AL'ADA DA HUKUNCE-HUKUNCENSA* tsira da amincin ubangiji su tabbata ga farin jakada babba dan Abdullah Muhammadur rasulullah (saw) bayan haka:

   Jinin Al'ada yana daga cikin al'amura muhimmai da ya kamata akula da su musamman a wannan lokacin da muke ciki zaka samu daga cikin "yan uwa mata suna jahiltar hukunce-hukuncensa abun da zai baka taqaici shine zaka samu daliba mai zuwa makaranta tana da matsala akan Al'adarta amma bazata iya tambayar malamintaba ko tasa a tambayar mata ko ta rubuta a takarda ko makamancin hakan saboda tana jin kunya muddun idan ba karatu ne ya biyo ta wajan ba sai taji hukuncin amma bazata taba tambayaba a haka zata cigaba da bautawa ubangijinta cikin jahilci to abun tambaya anan mai zuwa makaranta ma ta aikata hakan meye tunaninka da wacce da wacce bata taba zuwa ba? 

*Daga cikin abubuwan da zamu taqaita akansu sune kamar haka :

*1- Yaushe mata suka fara Al'ada*
*2- mene ne jinin Al'ada*
*3- meye hikimar da yasa mata suke jinin Al'ada*
*4- Ya ya launin jinin Al'ada yake*
*5-Daga wace shekara mata suka fara jinin Aal'ada*
*6- Tsawan wane lokaci. Jinin Al'ada yake dauka*
*7- Ta ya ya mace zata san jinin Al'ada zai zo mata*
*8- Ta ya ya mace zata san jinin Al'ada ya dauke mata*
*9- Mai mai tuwar jini Al'ada a wata sama da sau daya*
*10- Al'adar mace mai ciki*
*11- Abubuwan da suke bujurowa mace yayin da take Al'ada*
*12- Jinin Nifa'si (jinin haihuwa)*
*13- Tsawan wane lokaci jinin haihuwa yake dauka*
*14- Abubuwan da suke haramta akan mai Al'ada da mai jinin haihuwa*
*15- Mene ne jinin cuta*
*16- Meye hukuncin jinin cuta*
*17- Amfani da abun da zai hana zuwan jinin Al'ada*
*18- Amfani da abun da zai jawo zuwan jinin Al'ada*
*19- Amfani da abun da zai hana daukar ciki*
*20- Amfani da abun da zai zubar da ciki*
*21- Abubuwan da ake qirqirarwa mata masu jinin Al'ada da masu jinin haihuwa*
*22- Rufewa*

Wannan shi ne kadan daga cikin abubuwan da zamu tattaunawa akai in sha Allah 

Shi yasa muka ga da cewar mufassarasa cikin harshen hausa domin kowa da kowa ya iya karantawa asali mun rubuta littafin ne da larabci ba kuma kowa zai iya karantawa ba kuma muka ga da cewar mu watsasa ta wannan saha ta media kuma mu taqaitasa saboda ire-irena wadanda basa jure karanta dogon rubutu kuma in sha Allah zamu taqaitu wajan dauko maganganun da malamai suka rinjayar dasu/kuma dan Allah muna roqon duk wanda yaga mun kawo wata magana wacce bata ingantaba ko kuma kuskurene dan Allah ya sanar da mu wannan itace babbar qaunar da zai yi mana fatan Allah subhanahu wata'ala ya bamu da cewa ya tsakake mana ayyukanmu yasa mu amfanar da "Yan uwanmu mata har ma da mazan domin duk da cewar baka al'ada dole kana da masu Al'ada da suke zagaye dakai ko dai matarka ko "yayanka kuma kula da ibadarsu wajibine akan kuma sai Ubangiji ya tambayeka akai. 


*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi*
              *Nazifi Yakubu Abubakar*
               *Abu Rumaisa*
                🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)