KUNDIN MA'AURATA // 12

KUNDIN MA'AURATA // 12
.


ABIN DA KOWA YAKE GANI
Suna maganar dalilan dake sanya mace hauka ne a lokacin da kishi ya taso mata, sai suka ce: Mace kan miqa kanta ne kacokan ga namijin da zarar zuciyarta ta natsu da shi, wannan mutumin shi zai yi jagorancin rayuwarta gaba daya, ta yi hukuncin rayuwa da shi daga duniya har lahira, sai ya zamo yana da wani matsayi na yarda wanda ko mahaifinta bai samun irinsa, don akwai maganganun da in ba mijin ba ba za ta taba yi da wani ba, ita kenan, amma shi namijin da mace ta nuna tana qaunarsa kuma bai yi wani kokwanto ba wurin yarda da ci gaba da soyayya da ita qila don ya hango wani abu ne da ya burge shi wanda ido zai iya gani, shi ya sa in wasu abubuwa daga baya sun taso zai iya rabuwa da ita cikin sauqi ba tare da cutuwar zuciya sosai kamar macen ba, don tun farko bai ba da zuciyarsa gaba daya ba, gaskiya wannan nazari ne kawai.
.
Mace in namiji ya nuna qaunarta takan dan dakata ta lugwigwita maganar tukun na dan wani lokaci, ta sanya lamarin a cikin mizani ta gani anya wannan ba zai ci amanata ba? Matsalar kuma ba wasu hanyoyi take da su na gano cewa ba zai ci amanar tata ba sama da mu'amalarta da shi, wai tanan ne za ta fahimce shi, in ma uwarta ta nemi jin wasu 'yan abubuwa na sirri a tsakaninsu ba dole ne ta gaya mata ba, saboda tana ganin cewa wannan abu ne da ya shafi rayuwarta.
.
To in aka sami akasi sai ya yi mata mummunan tasiri, ya hana ta kwanciyar hankali, ta riqa ganin kanta tsirara a gaban mutane, ta tuna irin maganganun da aka gaya mata na ta bi da lura amma ta watsar, sai ta ji cewa a shirye take ta yi komai don rayuwarta ta riga ta lalace, to namiji a irin wannan matsayin ba kowa ba ne, duk lafazin da ba ka taba zato ba za ta ambato shi, ba ta damu da abin da zai biyo baya ba, wadanda za su iya magance lamarin su ne uwayenta, yadda za su jawo ta a jiki, su dauke hankalinta wajen nuna qaunarsu gareta gami da fada mata maganganu masu dadi, wadanda za su mantar da ita halin da ta shiga.
.
Sai dai kuma uwaye ba su cika yin hakan a irin wannan lokacin ba, kodai don barinta ta dandani abin da ta janyo da hannunta, ko kuma saurarawa har lamarin ya dan yi sauqi, ita kuwa a daidai wannan lokacin za ta fara neman mafita, wata za ta yanke hukuncin cin mutuncin mijin ne ta kowace hanya, albashi duk abin da zai faru ya faru, wata kuma sai ta daura kaifukan gaba daya a kan wace za a auro, ta ga cewa ita ce take nema ta qwace mata jin dadinta don haka sai dai Allah ya raba su, za ta fuskance ta da duk abin da take da shi.
.
Abubuwan da suka bayyana a irin wannan matakan da ake dauka su ne ake kira kishi, in dai haka ne to ba dole ne ya bayyana ga namiji ba, sau daya na ga wani mutum da matarsa take koyarwa a wata makarantar furamare wanda suka kwashe shekaru da dama suna tare, sai dai duk dadewannan suna dan samun wasu 'yan matsaloli a tsakaninsu, in kuma an samu din wani abokin aikinta ne yake shiga tsakaninsu, domin mijin har makarantar yake biyo ta, da wannan sai abokin aikin ya zama cikakken alqalin da su biyun duka suka yarda da shi, don yakan kebe da kowa ya gaya masa laifinsa, ya kuma ja hankalinsa, ya gaya masa maganganu masu dadi yadda zai haqura ya ci gaba da zama da masoyinsa cikin kwanciyar hankali.
.
To bayan wasu shekaru sai zaman ya gagara gaba daya, har dai aka haqura da auren kowa ya kama gabansa, amma abin da zai daure kai shi ne, alqalin da yake shiga tsakani kuma shi ne ya fito a matsayin manemi, da bincike ya yi nisa an gano cewa tsohuwar matarsa ce ta nuna qaunar abokin aikin nata a sakamakon irin ban bakin da yake mata, da irin qoqarin da yake yi na ganin sun zauna lafiya, tanan ne qaunarsa ta kurdada zuciyarta, wancen auren na qarewa kuma ta ga ba wanda ya dace ta zauna da shi in ba abokin aikin ba, shi kuma tsohon mijin ya maka su a kotu kan cewa bai tarda ba, yana ganin dan tsakiyannan shi ne ya fitar masa da mata don ya sami damar aure masa ita.
.
A qarshe dai ya fadi a gaban alqali cewa bai damu ba kowa ya aure ta amma ba wannan dan tsakiyan ba, shi kuwa abokin aiki tunda ya ga mata fara sal kyakkyawa wace bai taba zaton zai iya neman irinta ba ta nuna tana son shi sai kawai ya miqa wuya, a dalilin rashin samun abin da zai hana shi nemanta, alqalima ya tambayi tsohon mijin in shi ne ya rabu da matar ya ce "I", ya sake tambayarsa in yana da haqqin sai ya yarda da mutum kafin tsohuwar matar tasa ta aure shi, ya ce "A'a" daganan aka watsar da qarar saboda rashin hujjar yinta.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)