MU YI HATTARA!

As Received:
“MU YI HATTARA!

Wani bawan Allah ya turo mun wannan ta WhatsApp kuma naga muhimmancin ni ma in yaÉ—a

Ababe goma sha biyu (12) da ya kamata muyi takatsantsan da su!

Sakamakon lokaci da ya canza, rashin gaskiya na ƙara yawaita, zalunci yana cigaba da samun wurin zama a zuciyoyin mutane, Yaudara, matsalar sace sace da garkuwa da mutane ta zama ruwan dare game duniya. Ya kamata kowa yayi hattara da waɗannan ababe.


1. Sayen Simcard mai rigister ko layin Data. Duk simcard da ya kasance ba kai kayi masa rigista da sunanka ba, ka yi hattara kar ka saka shi a wayarka. Domin musibar da hakan ka iya ja yo maka, baka ji baka gani ba.

2. Yi hattara da sayen second-hand É—in wayar hannu. Idan kuma baka da halin sayin sabuwar waya, to ka sayi second a wurin wanda yake da shago, a kuma baka kwalinta na É—auka da risiti. Ko da wani abun na iya tasowa.

3. Duk wanda ya kira ka da dare yace maka shi direba ne an bashi saƙo ya kawo maka. Alhali kai kasan dacewa babu wani saƙo da kake tsammanin a aiko maka, to rufawa kanka asiri ka zauna gidanka, kuma ka cigaba da addu'a.

4. Hattara da majalisu da teburan masu shayi. Kasan irin labarin da ke fitowa bakin ka, a lokacin da kake cikin jama'a. Mafi yawa miyagun anan suke zama kuma wani abun daga irin waÉ—annan wuraren ake kulla shi.

5. Yi hattara da 'yan matan da kuke haɗuwa a social media, Ke ma yar uwa yi hattara da mazan da kuke haɗuwa da su a social media. bakasanta ba baka san inda tafito ba, kema baki san shi ba, bakisan inda ya fito ba, ku ƙulla soyayya har a nemi ɗaya daga cikinku yayi tattaki zuwa wani wuri domin ku haɗu. A yi takatsantsan kwarai wajen kulla irin wannan alaka, kuma a zurfafa bincike.

5. Yi iya yinka wajen siririnta samunka ko wani alhairi mai girma da ya sameka a cikin zuciyarka. Da yawa waÉ—anda muke tare dasu, su ake haÉ—a baki da su wajen cutar damu! Kuma da yawa daga cikin mutanen da muke zaune da su basa farin ciki da cigaba ko wani alhairi a rayuwarmu, don haka a sirranta cigaba kowani babban alhairi da ka samu, sai abinda ya zama tilas a sani. Kada aba mai hassada ko kyashi damar ganin abin da zai sa shi yayi hasadar.

6. A cikin wuraren da kake tafiya wurin neman abinci, ka dinga sauya lokaci ko rana, kada ka mayar da wata hanya ko lokaci ya zama na dindindin na gabatar da hidimominka na rayuwa!

7. Zamani ya samar da cigaba sosai kar ka bari a barka a baya. Idan kana da hali ka saka camera ta CCTV a masana'antarka da harabar gidanka, suna matukar taimakawa bincike ko da wani tsautsayi ya faru.

8. Duk abin da ka gani wanda baka natsu da shi ba, da ya shafi tsaro ko illata lafiya, ka kai rahotonsa ga hukumomin da ya dace nan take.

9. A hir, da yin ƙaryar arziki. Kana rayuwar ƙarya da nuna isar abin da baka mallaka ba. A kaikaice kana jifa kanka cikin musiba ne baka sani ba. A tafi neman ƙiba a dawo da rama!

10. Duk wani zikiri da kake da tabbacin ya samo asali daga Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata gare shi, ko wata addu'a ta neman tsari. To ka rike kuma ka dage ba fashi. Azkar na bayan sallar Asuba da tsakanin Sallar Magariba zuwa Isha'i ba lokacin wasa bane ko shashanci, dage ka nemi tsari daga wurin Ubangiji.

11. Ka guji cuta ko zaluntar mutane ko tauye dukiyarsu, mu guji cin haram da ciyar da 'yayanmu daga haram. Matuƙar babu hakkin mutane a kan ka, cikin ikon Ubangiji sai kaga ka samu kariya.

12. Duk inda kaji ana gabatar da wani bayani da ya shafi harkar tsaro ko lafiya, yi ƙoƙari ka tsaya ka saurara, insha Allahu ba zaka rasa samun darasin da zaka ɗauka ba.

Daga ƙarshe musan cewa babu wani mai iya bamu kariya bayan Allah maɗaukakin sarki, don haka mu guji saɓa masa mu kuma kiyaye dokokinsa, sai ya kiyayemu. Aameen yahayyu yaqàyyum bi rahma Tika Aztagiz🤲🤲

Kukan kurciya!!!
*COPIED*
Post a Comment (0)