LABARI
Yana zaune a gida sai ga wayar dan uwansa, yana gaya masa cewa za su kawo masa ziyara shi da iyalinsa.
Da yake ana cikin wani yanayi na hakuri, kuma ga mai gidan ba ta nan, amma ai duk da haka, sada zumunci yada albarka ne, kuma babbar ibada ce.
Ya leka ya leko, Allah Ya agaje shi ya sami lemo har kofi biyu, ya yi shukura ga Allah ya shirya tarben baki.
Can sai ga su a bakin kofa sun iso, ya tashi cikin karsashi da farin ciki ya bude kofa, cikin bazata.sai ya ga su uku ne; ga danuwansa da matarsa ga karin surukar dan uwansa!!!
Nan lissafin lemon tarba ya canja, amma ya yi ta maza, ya tarbe su, ya yi musu maraba da kyau.
Ya shiga dakin girki ya sanya lemukan biyun a kan tire, sannan ya zubo ruwa a daya kofin.
Ya kawo wa baki; ya ajiye lemo a gaban surukarsu da matar dan uwansa, shi kuma dan uwansa ya ajiye Masa ruwa ya ce: Na san kana son Sprite shi ya sa na kawo maka shi.
Dan uwansa na sha sai ya ji a she ruwa ne. Sai surukar ta ce: Ai kuwa na fi son Sprite din ma. Sai dan uwansa ya tashi ya ce: Bari na je dakin girki na sanya maki a sabon kofi. Can sai suka ji: Tartsatsa! Kofin gilashi ya fashe.
Danuwan ya dawo, ya ce: Subhanallah! Ai kofin ya subuce ya.fadi ya fashe. Sai ta ce: Ba rabo ba.
Suka sha aka yi hira suka tashi don su koma. Matan sun yi gaba Sai dan uwan ya gaisa da danuwansa musafaha, ya sanya masa dunkulen kudin a hannunsa ya ce: Wannan a wanke Sprite da ya zube a dakin girki, mun gode kwarai da gaske.
NB: Bai yarda ya tona asirin dan uwansa ba, ballantana ya kunyata shi.
Shin irin wannan dan uwa zai iya kunyata iyayensa kuwa??
Na karanta ne ya burge, na rubuta shi a haka.
From Mal
✏️ Dr. Abdulkadir Ismail
Sautussunnah.com
Telegram channel
https://t.me/joinchat/9TvvzkBkxKtjZGJk